A'isha Buhari: Dalilin da ya sa na wallafa bidiyon Pantami yana rusa kuka yayin wa'azi

A'isha Buhari: Dalilin da ya sa na wallafa bidiyon Pantami yana rusa kuka yayin wa'azi

  • Mai dakin shugaban kasan Najeriya, Aisha Buhari ta bayyana dalilin da ya sa tayi amfani da bidiyon ministan sadarwa Ali Isa Pantami wurin bayani ga 'yan Najeriya
  • A cewar ta ta wallafa bidiyon ne don kwatanta wa ‘yan Najeriya abubuwan da suke faruwa dangane da yaƙi kan rashin tsaron da ke kasa
  • Aisha Buhari ta wallafa bidiyonsa ne yayin da yake wa’azi yana rusa kuka saboda kashe-kashen da ake yi a lokacin mulkin Goodluck Jonathan

FCT, Abuja - Uwar gidan shugaban Buhari, Aisha Buhari ta bayyana kwararan dalilan ta na amfani da bidiyon ministan sadarwa, Ali Isa Pantami don kwatanta wa ‘yan Najeriya abubuwan da suke faruwa na matsalolin rashin tsaro a kasar nan.

Kara karanta wannan

An saki bidiyo yayin da kwamandan IPOB/ESN Shakiti-Bobo ya ambaci sunan mai daukar nauyin kungiyoyin

Matar shugaban kasan ta wallafa bidiyon ministan wanda dama malamin addinin musulunci ne yana koyar da mutane tare da yin wa’azi dangane da kashe-kashen da ake yi a Najeriya.

A'isha Buhari: Dalilin da ya sa na wallafa bidiyon Pantami yana rusa kuka yayin wa'azi
First Lady ta Nigeria, Aisha Buhari. Hoto: Aisha Buhari
Asali: Instagram

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wallafa bidiyon da yin tsokaci akan shi ya janyo cece-kuce sosai

Kamar yadda Aisha Buhari tayi tsokaci akan bidiyon Pantami a wallafar ta ta ranar Lahadi inda ta sa:

“A cire tsoro a yi abinda ya kamata”.

Wannan wallafar ta janyo cece-kuce inda har wasu suke cewa tana bayyana gazawar mulkin mijinta kamar yadda ta dade tana yi tsawon shekaru

Bayan surutai sun yawaita ne ta kara wata wallafar yayin da ta faɗaɗa bayani dangane da wallafar ta ta farko. Ta ce ta yi amfani da bidiyon ne don ta bayyana yadda yin abinda ya dace ba tare da tsoro ba yake haifar da da mai ido.

Kara karanta wannan

Hukuncin da Ya Dace Yan Najeriya Su Ɗauka Kan Shugabannin da Suka Gaza Cika Alƙawari, Tsohon Ministan Sadarwa

Kamar yadda Aisha Buhari ta yi wallafar ta biyu a ranar Litinin, a shafinta na Instagram:

“Tafsir din Malam akan tsoron Allah ba na mutum ba. Bayan an cire tsoro da son kai an shiga Zamfara, abubuwa sun fara kyau, sai a dage a shiga sauran wurare haka”

Ba wannan ne karo na farko da Aisha Buhari ta fara sanya baki mulkin Buhari ba

Ba yau ne Aisha Buhari ta fara tsoma bakin ta a matsalolin gwamnati ba, tun 2016 ta taba bayyana yadda wasu mutane suke mulkar kasa ba shugaba Buhari ba.

A lokacin maganar ta janyo cece-kuce iri-iri inda wasu suke cewa ta fi kowa kusanci da shugaban kasa don haka ta fi kowa fahimtar abinda yake faruwa.

A 2019 ta kara magana akan yadda wasu mutane suke bin umarnin Garba Shehu maimakon su bi na mijin ta.

A watan Disamban da ta gabata aka fara samun jita-jita akan yadda ta tsere kasar Dubai saboda tsananin rashin tsaron Najeriya amma daga baya BBC ta gano cewa ta je Dubai ta yi watanni da dama amma wani dalilin na daban ne ya kai ta.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel