APC ta kare Buhari, ta fadi dalilan gwamnatin tarayya na karbo bashin tiriliyoyi bini-bini

APC ta kare Buhari, ta fadi dalilan gwamnatin tarayya na karbo bashin tiriliyoyi bini-bini

  • Jam’iyyar APC ta bayyana abin da ya sa Gwamnatin Tarayya ke karbo bashi
  • John James Akpanudoedehe yace ana aro kudi ne domin ayi wa al’umma aiki
  • Sakataren na APC yace a lokacin PDP ne aka rika aro kudi, wasu na sace wa

Abuja - Jam’iyyar APC mai mulki tace gwamnatin Muhammadu Buhari tana karbo bashi ne domin ta iya aiwatar da ayyukan da ke cikin kasafin kudin 2021.

A wani jawabi da sakataren rikon kwarya na jam’iyyar APC, Sanata John James Akpanudoedehe, ya fitar, ya kare gwamnatin tarayya da mutane suke ta suka.

Daily Trust ta rahoto John James Akpanudoedehe yana cewa abubuwan more rayuwa da ake gina wa suna taimaka wa wajen farfado da tattalin arzikin kasar.

Kara karanta wannan

Ambaliyar ruwa ya gangara da motoci, ya hallaka mutane da yawa a Abuja

Sanata Akpanudoedehe yace ayyukan sun taimaka wajen samar da ayyukan yi ga al’umma, ya rage talauci, sannan ya inganta jin dadi da rayuwar mutane.

Sakataren jam’iyyar APC na riko ya yi wannan jawabi ne a matsayin martani ga PDP da ta soki shugaba Muhammadu Buhari saboda yunkurin sake cin bashi.

Buhari
Shugaban kasa Buhari Hoto: www.channelstv.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

John James Akpanudoedehe ya cacaccaki PDP

“A maimakon lokacin PDP, kudin da ake cin bashi yanzu za su yi amfani ne wajen cike gibin da ke cikin kasafin kudin 2021 domin ayi nasarar dabbaka tsare-tsaren farfado da tattalin arziki.”
Tsare-tsaren tattalin arzikin za su taba bangarorin gina abubuwan more rayuwa, bunkasa kiwon lafiya, karfafa sha’anin gona, samar da isasshen abinci, samar da wuta, sannan a yaki COVID-19.”
“Ana cin bashi ne domin ayi abubuwan da ake matukar bukata, sua zama tilas wajen gyara tattalin kasa da nufin gwamnati ta inganta halin da al’umma ke ciki.”

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Hon. Elumelu ya bayyana Gwamnan da zai iya hambarar da APC daga kan mulki

“A mulkin PDP ne aka ci bashi da sunan za a gyara wuta, saye makaman yaki da a’addanci, amma aka karkatar da kudin, aka yi ayyukan da ke gaban PDP.”
“Kudin da aka ci bashi suka kare a aljihun dangi da iyalin masu mulki. Har yau Najeriya na biyan bashin $460m da aka ci da sunan za a kafa CCTV a Abuja.”

APC tace gwamnatin PDP ta jefa Najeriya a duhu, sai yanzu Buhari yake kokarin shawo kan kasar.

Bashi na neman yi wa Najeriya yawa?

Kwanakin baya aka ji babban bankin Duniya suna nuna cewa bashin biliyoyin dalolin kudin da ake bin gwamnatin Najeriya da wasu kasashe tara ya yi yawa.

Alkaluman ofishin bashi na kasa watau DMO, sun tabbatar da cewa zuwa karshen watan Mayun 2021, Najeriya ta karbi aron Dala biliyan 11.51 daga bankin Duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng