Wata sabuwa: Jam'iyyar APC ta fatattaki tsohon gwamna da wasu mambobi 40

Wata sabuwa: Jam'iyyar APC ta fatattaki tsohon gwamna da wasu mambobi 40

  • Rahotanni daga jihar Enugu na bayyana cewa, APC ta kori wasu mambobinta bisa saba dokar jam'iyya
  • Rahoto ya ce, mutane 41 ne jam'iyyar ta kora bisa laifin kai karar shugabanta kotu ba bisa ka'ida ba
  • Daga cikin wadanda aka kora, akwai tsohon gwamna da wasu sauran jiga-jigan siyasa a jihar ta Enugu

Enugu - Akalla jiga-jigan jam’iyyar APC na jihar Enugu 41 aka kora daga jam’iyyar mai mulki a ranar Lahadi, 12 ga watan Satumba, sakamakon zargin karya tsarin dokar cikin gida.

A jawabinsa ranar Lahadi ga manema labarai kan matakin hukunta mambobin, shugaban kwamitin riko na APC a jihar, Ben Nwoye, ya ce mutanen da abin ya shafa sun shigar da kara a kan jam'iyyar ba tare da fara bin hanyoyin magance rikici ba a cikin gida ba.

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

Leadership ta rahoto cewa mambobin sun shigar da kara a babbar kotun tarayya da ke Abuja suna neman a cire Nwoye daga mukaminsa.

  1. Sai dai shugaban ya bayyana cewa wadanda aka kora daga aikinsu ya sabawa sashi na 21 (D), sashe na V na kundin tsarin mulkin APC, in ji Vanguard.
Yanzu-Yanzu: Jam'iyyar APC ta fatattaki tsohon gwamna da wasu mambobi 40
Jam'iyyar APC | Hoto: vamguardngr.com
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Da yake ambato abin da kundin tsarin mulkin APC ya tanadar kan batun, ya ce:

“... duk wani mamba da ya shigar da kara a gaban kotu kan jam’iyya ko wani jami’inta a kan duk wani al’amari da ya shafi aiwatar da ayyukan jam’iyyar ba tare da fara bin hanyoyin gyara da aka tanada a cikin wannan Tsarin Mulki ba. an kore shi kai tsaye daga jam'iyyar ..."

Jiga-jigan jam'iyyar APC da aka kora

Wadanda jam'iyyar ta kora a jihar sun hada da:

Kara karanta wannan

Coci ya ruguje kan masu bauta ana cikin ibada a Taraba, ya hallaka mutane biyu

  1. Tsohon gwamnan soja, Group Capt Joe Orji
  2. Tsohon kakakin majalisar dokokin jihar, Hon. Eugene Odo,
  3. tsohon mataimakin dan takarar gwamna na jam'iyyar, Prince Chikwado Chukwunta,
  4. Gen. J.O.J Okoloagu, tsohon dan majalisar wakilai
  5. Chukwuemeka Ujam da dai sauran wasu 36 na jam'iyyar

Babbar magana: 'Yan APC sama da 50,000 sun sauya sheka zuwa PDP a Adamawa

A wani labarin, Sama da mambobin jam’iyyar APC 50,000 ciki har da tsohon sakataren gwamnatin jihar Adamawa, Mista Kobis Ari Themnu, sun koma PDP a ranar Asabar, 4 ga watan Satumba.

Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar wanda ya tarbe su a dandalin Ribadu Square na taro a Yola ya zarge su da yin imani da kuma daidaita amincin su ga jam'iyyar da ta gaza tun farko, inji rahoton jdairdar Leadership.

Sai dai Atiku ya ce kuskuren su na kasancewa a cikin APC yanzu an gafarta musu, sannan ya kara tabbatar da cewa PDP ta shirya ta karbi mulkin kasar nan a zaben 2023.

Kara karanta wannan

Ya dawo da kafar dama: Ronaldo ya zura biyu yayinda Manchester ta narki Newcastle 4:1

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.

Online view pixel