Da dumi-dumi: Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya bar Najeriya don halartan taro mai muhimmanci

Da dumi-dumi: Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya bar Najeriya don halartan taro mai muhimmanci

  • Jirgin mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya bar Abuja zuwa Jamhuriyar Guinea don halartan babban taron shugabannin ECOWAS
  • Osinbajo zai wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari a taron wanda zai gudana a yau Alhamis, 15 ga watan Satumba
  • Zai samu rakiyar karamin ministan harkokin waje, Ambasada Zubairu Dada

Abuja - Mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo zai wakilci shugaban kasa Muhammadu Buhari a babban taro na musamman na shugabannin kasashe da gwamnatocin ECOWAS kan yanayin siyasa a Jamhuriyar Guinea.

Babban mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai na ofishin mataimakin shugaban kasa, Mista Laolu Akande ne ya bayyana hakan da safiyar Alhamis, 16 ga watan Satumba, jaridar The Nation ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: Hotuna sun bayyana yayin da Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinonin INEC

Da dumi-dumi: Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya bar Najeriya don halartan taro mai muhimmanci
Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya bar Najeriya don halartan taron shugabannin ECOWAS Hoto: Yemi Osinbajo.
Asali: Facebook

A makon da ya gabata, Osinbajo ya halarci babban taron ECOWAS na baya kan yanayin siyasa a Guinea da Mali.

An gudanar da taron ne ta yanar gizo a ranar 8 ga watan Satumba.

Taron na zahiri da zai gudana a ranar Alhamis zai sake nazarin halin da ake ciki a Guinea dangane da rahoton babban taron ECOWAS zuwa Conakry.

Mataimakin shugaban kasar, wanda ya bar Abuja da safiyar yau, zai samu rakiyar karamin ministan harkokin waje, Ambasada Zubairu Dada kuma ana sa ran zai dawo Abuja daga baya a ranar Alhamis, jaridar Punch ta kuma ruwaito.

Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya bayyana wadanda ke ingiza rashin tsaro a Najeriya

A wani labari na daban, mun ji a baya cewa Farfesa Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban Najeriya a ranar Alhamis, 9 ga watan Satumba, ya zargi manyan Najeriya da ingiza rashin tsaro a kasar.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Najeriya na shawarar baiwa Fursunoni damar jefa kuri'a a zaben 2023

Jaridar Punch ta rahoto cewa ana ingiza rashin tsaro a cikin kasar ta hanyar nuna kabilanci, ayyuka da maganganun tunzurawa.

Legit.ng ta tattaro cewa Osinbajo yayi magana ne a wani taron karramawa a Cibiyar Taro ta kasa da kasa, Abuja mai taken: "Rashin tsaro na ƙasa da yanki: Matsayin 'yan siyasa da waɗanda ba na siyasa ba wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin gwiwa."

Shugaba Buhari ya ba Osinbajo shugabancin kwamitin da zai gyara kiwon lafiya a jihohi 36

Legit.ng ta kuma rahoto a baya cewa, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kafa kwamitin da zai fitar da tsare-tsare da dabarun gyara sha’anin kiwon lafiya a Najeriya.

Mai magana da yawun bakin shugaban Najeriyar, Malam Garba Shehu ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar a ranar 6 ga watan Satumba, 2021.

Kamar yadda kuka samu labari a baya, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne zai jagoranci wannan kwamiti da zai yi wannan babban aiki.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun banka wuta gidan Kakakin majalisar wakilan jihar Zamfara

Asali: Legit.ng

Online view pixel