Da dumi-dumi: Hotuna sun bayyana yayin da Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinonin INEC

Da dumi-dumi: Hotuna sun bayyana yayin da Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinonin INEC

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinoni uku a hukumar INEC makonni bayan majalisar dattawa ta tabbatar da su
  • Sabbin kwamishinonin sun hada da Baba Bila daga arewa maso gabas, Sani Adam daga arewa maso tsakiya da Abdullahi Abdu daga arewa maso yamma
  • Bayan rantsarwar, shugaban kasar ya kira taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) na mako-mako a fadar gwamnati

Aso-Rock, Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar Laraba, 15 ga watan Satumba ya rantsar da sabbin kwamishinoni guda uku na hukumar zabe mai zaman kanta (INEC).

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa an gudanar da bikin ne a takaice kafin fara babban taron majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) na mako a fadar shugaban kasa dake Abuja.

Da dumi-dumi: Hotuna sun bayyana yayin da Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinonin INEC
Buhari ya rantsar da sabbin kwamishinonin zaben guda uku Hoto: Buhari Sallau.
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa wadanda aka rantsar sun hada da Dr Baba Bila mai wakiltar shiyyar arewa maso gabas, Farfesa Sani Adam, arewa maso tsakiya da Farfesa Abdullahi Abdu, mai wakiltar arewa maso yamma.

Kara karanta wannan

Jerin fitattun 'yan Najeriya 4 da Buhari zai iya nadawa a matsayin sabon ministan noma

Rahoton ya ce a halin yanzu shugaban kasar yana jagorantar taron FEC na mako a dakin taro na ofishin Uwargidan Shugaban kasa a Fadar Shugaban Kasa.

Channels TV ta kuma ruwaito cewa Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo (SAN) da Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Boss Mustapha, na cikin wadanda ke halartar taron a zahiri.

Akwai kuma ministan yada labarai da al’adu, Lai Mohammed; babban lauya kuma ministan shari'a, Abubakar Malami; da ministan albarkatun ruwa, Suleiman Adamu.

Sauran sun hada da ministocin kudi, kasafin kudi da tsare -tsare na kasa, Zainab Ahmed; ayyuka da gidaje, Babtunde Fashola (SAN) da na harkokin cikin gida, Ogbeni Rauf Aregbeshola.

Shugabancin 2023: Okonjo-Iweala, Peter Obi da wasu 'yan siyasa 16 na kudu maso gabas da aka nemi suyi takara

Kara karanta wannan

NYSC za ta zakulo hazikan mambobin bautar kasa don tsoma su a harkar fina-finai

A wani labarin, mun ji cewa kiraye-kiraye da ake yi na neman shugaban kabilar Ibo a 2023 ya dauki saon salo a ranar Litinin, 14 ga Satumba, yayin da kungiyar Umunna Lekki Association (ULA) ta lissafa wadanda ka iya zama 'yan takara daga jihohin kudu maso gabas biyar.

Jaridar Guardian ta rahoto cewa ULA, wacce ta kunshi matasa 'yan kasuwa daga kasar Igbo mazauna Lekki, Ikoyi, Banana Island, Victoria Garden City (VGC) da Victoria Island na jihar Legas, ta bayyana shirinta na tallafawa shugabancin Igbo da kudaden su.

Legit.ng ta tattaro cewa a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun shugabanta, Ikem Umeh-Ezeoke, ULA ta fitar da jerin fitattun yan kabilar Igbo maza da mata wadanda za su iya juya arzikin kasar nan.

Asali: Legit.ng

Online view pixel