Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya bayyana wadanda ke ingiza rashin tsaro a Najeriya

Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya bayyana wadanda ke ingiza rashin tsaro a Najeriya

  • Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya zargi fitattun 'yan Najeriya a matsayin manyan masu ingiza rashin tsaro a kasar
  • Osinbajo ya yi jawabi a wurin wani taron karramawa a Cibiyar Taro ta kasa da kasa (ICC), Abuja
  • A cewarsa, za a magance matsalar rashin tsaro a kowane yanki na kasar idan manyan mutane da sauran 'yan Najeriya suka dawo kan matsaya guda

FCT, Abuja - Farfesa Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban Najeriya a ranar Alhamis, 9 ga watan Satumba, ya zargi manyan Najeriya da ingiza rashin tsaro a kasar.

Jaridar Punch ta rahoto cewa ana ingiza rashin tsaro a cikin kasar ta hanyar nuna kabilanci, ayyuka da maganganun tunzurawa.

Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya bayyana wadanda ke ingiza rashin tsaro a Najeriya
Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya bayyana cewa manyan mutane ne ingiza rashin tsaro a Najeriya Hoto: Yemi Osinbajo.
Asali: Facebook

Legit.ng ta tattaro cewa Osinbajo yayi magana ne a wani taron karramawa a Cibiyar Taro ta kasa da kasa, Abuja mai taken: "Rashin tsaro na ƙasa da yanki: Matsayin 'yan siyasa da waɗanda ba na siyasa ba wajen tabbatar da zaman lafiya da haɗin gwiwa."

Kara karanta wannan

2023: Babu Amfanin Sake Komawa Matacciyar Jam'iyya, Sanata Ya Soki Yan Siyasa

Osinbajo ya ce sukar da masu fada aji ke yi kan ayyukan gwamnati ba tare da la’akari ba su ne ke rura wutar fitina da tayar da kayar baya.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kara da cewa za a magance matsalar rashin tsaro a kowane bangare na kasar idan manya da sauran ‘yan Najeriya suka dawo kan yarjejeniya.

Mataimakin shugaban kasar ya jaddada cewa fitattun mutane ba su kyautawa idan aka zo kan batun magance matsalar rashin tsaro.

Ya ce:
“Wasu daga cikin fitattun ba za su iya cimma matsaya ba game da rashin tsaro. Yawancin fitattun da ke tallata ajandar kabilanci sun dogara ne da ayyukan da ba na gaskiya ba wajen haɓaka bangaranci da ƙabilanci. Manyan mutane suna amfani da wannan don ci gaban kansu.
"Ko dai saboda son kai ko rashin sanin yakamata ba su iya gina yarjejeniya ta zamantakewa da siyasa wacce al'umma mai adalci da tsari za ta iya farawa. Suna ingiza gabar kabilanci da na addini.”

Kara karanta wannan

Ku koyi sana'a babu aikin da gwamnati za ta baku, inji wani sanata ga 'yan NYSC

Rashin tsaro: Wuta ‘yan bindiga za su, fadar Shugaban kasa ta mayar da martani ga Sheikh Gumi

A wani labarin, hadimin shugaban kasa Muhammadu Buhari, Femi Adesina, ya kalubalanci fitaccen malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi, kan cewa da yayi farmakin da sojoji ke kaiwa zai kara munana ta'addanci a Najeriya.

Adesina a cikin wani wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Alhamis, 9 ga watan Satumba ya bayyana Gumi a matsayin “mai son fashi da makami."

Duk da bai ambaci sunan Gumi ba, Adesina ya nakalto bayanin malamin a sarari, yana mai lura da cewa matsayin Gumi akan harin bam da sojoji suka kai wa 'yan bindigan karya ne.

Asali: Legit.ng

Online view pixel