Shugaba Buhari ya ba Osinbajo shugabancin kwamitin da zai gyara kiwon lafiya a jihohi 36
- Gwamnatin Tarayya ta kafa wani kwamiti da zai gyara sha’anin kiwon lafiya
- Farfesa Yemi Osinbajo ne wanda aka ba nauyin shugabantar wannan kwamiti
- Okowa, Sani Aliyu, Mairo Mandara suna cikin wadanda aka zaba a kwamitin
Abuja - Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kafa kwamitin da zai fitar da tsare-tsare da dabarun gyara sha’anin kiwon lafiya a Najeriya.
Mai magana da yawun bakin shugaban Najeriyar, Malam Garba Shehu ya bayyana wannan a wani jawabi da ya fitar a ranar 6 ga watan Satumba, 2021.
Kamar yadda kuka samu labari a baya, mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ne zai jagoranci wannan kwamiti da zai yi wannan babban aiki.
Kwamitin zai hada kai da gwamnatocin jihohin kasar nan da kuma shugabannin birnin tarayya Abuja.
An kafa wannan kwamiti ne bayan wani aiki da Vesta Healthcare Partners da ma’aikatar lafiya ta yi, ta bada shawarar yadda gwamnati za ta inganta lafiya.
Su wanene 'yan kwamitin?
Vanguard tace kwamitin mai kunshe da malaman asibiti, masana, kwararru, ma’aikatan gwamnati, wakilan NGF da majalisa zai yi aikin wata shida.
Sauran ‘yan kwamitin su ne; gwamnan jihar Delta, Dr. Ifeanyi Okowa, Dr. Osagie Ehanire, Cif Alex Okoh, Farfesa Ibrahim Abubakar, Babatunde Irukera.
Sai kuma; Ibrahim Yahaya Oloriegbe; Dr. Adedamola Dada; Dr. Sani Aliyu; Dr. Mairo Mandara; Dr. Haliru Yahaya, Dr Faisal Shuaib, sai Dr Gambo Aliyu.
Har ila yau akwai Farfesa Nasiru Sambo; Farfesa Uche Amazigbo; Dr Ifedayo Morayo Adetifa;
A kwamitin akwai Uche Amazigbo, Dr Betta Edu, shugabannin kungiyoyin NMA, PSN, NANNM da WHO.
Duk a makon nan ne kuma aka ji cewa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Dr. Ifedayo Morayo Adetifa a matsayin Darekta Janar na NCDC .
Dr. Adetifa Morayo Adetifa ya yi digirinsa na farko a jami’ar Ilorin, jihar Kwara a bangaren ilmin likitanci. Daga baya ya yi M.Sc da PhD a jami'ar Amsterdam.
Asali: Legit.ng