Gwamnatin Najeriya na shawarar baiwa Fursunoni damar jefa kuri'a a zaben 2023

Gwamnatin Najeriya na shawarar baiwa Fursunoni damar jefa kuri'a a zaben 2023

Gwamnatin Najeriya na shawaran baiwa fursunoni dake gidajen yari a fadin tarayya daman musharaka a zaben kasa na 2023.

Sakataren ma'aikatar harkokin cikin gida, Dr Shuaib Belgore, ya bayyana hakan ne yayinda yake karban bakuncin kungiyar rajin kare hakin fursunoni Carmelite Prisoners’ Interest Organisation, CAPIO, ranar Talata a Abuja.

CAPIO ta kaddamar da tsarin taimakawa Fursunoni wajen tilastawa gwamnati baiwa Fursunoni hakkinsu na zabe a Najeriya.

Mambobin CAPIO sun garzaya ofishin Sakataren ne domin neman taimako wajen aiwatar da wannan abu, rahoton DN.

Gwamnatin Najeriya na shawarar baiwa Fursunoni damar jefa kuri'a a zaben 2023
Gwamnatin Najeriya na shawarar baiwa Fursunoni damar jefa kuri'a a zaben 2023 Hoto: Nigerian Correctional Service NCS
Asali: UGC

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Sakataren, Shuaibu Belgire, ya bayyana cewa matsalar da suke fama shine yan bindiga na kai hare-hare gidajen gyara hali tare da sakin fursunoni.

Kara karanta wannan

Da duminsa: 'Dan gwamnan Kano AbdulAziz Ganduje ya kai karar mahaifiyarsa Goggo wajen EFCC

A cewarsa, wannan ne abu daya da ka iya zama matsala ga iya amincewa fursunoni kada kuri'a.

Yace:

"Yan ta'adda na kaiwa gidajen yarinmu hari. Abinda ya zama ruwan dare kuma hakan zai iya hana baiwa mutane daman shiga (gudanar da zabe)."
"Idan babu wannan matsalan, zamu yi aiki tare da ku domin baiwa fursunoni hakkinsu na zabe."

Shugaban kungiyar CAPIO, Rev. Fr Jude Isiguzo, ya bayyana cewa gwamnatin kasar Jamus ke daukan nauyin wannan gwagwarmaya tasu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdul Rahman Rashid avatar

Abdul Rahman Rashid Rashidah Abdul Rahman 'yar jarida ce kuma dalibar ilimi wacce ta kwashe shekaru kimanin hudu yanzu tare da shararriyar jarida Legit. Ta samu gogewa a ɓangaren rubutun labarai akan fannoni shatta, wanda suka hada da siyasa, kasuwanci, wasanni, nishadi, dss. Zaku tuntubarta a akwatin email: abdulrahman.rashidah@corp.legit.ng