Gwamnatin Buhari: Ba zamu iya kin yafewa 'yan bindiga ba, su ma 'yan Najeriya ne

Gwamnatin Buhari: Ba zamu iya kin yafewa 'yan bindiga ba, su ma 'yan Najeriya ne

  • Gwamnatin shugaba Buhari ta bayyana cewa, za ta ci gaba da yafe wa 'yan ta'adda idan suka mika wuya
  • Ministan harkokin 'yan sanda, Muhammad Dingyadi ne ya bayyana haka yayin wata tattaunawa
  • Ya kuma bayyana cewa, sojoji na ci gaba da aiki tukuru don ganin sun gama da sauran 'yan ta'adda masu taurin kai

Gwamnatin Tarayya ta ce ba za ta rufe kofar tuba ba ga 'yan bindigan da suka mika wuya da sunan tuba, Daily Trust ta ruwaito.

Ministan Harkokin 'Yan Sanda, Muhammad Dingyadi, ya bayyana hakan ne lokacin da ya bayyana a shirin Politics Today, na gidan Talabijin na Channels, a daren Talata 14 ga watan Satumba.

Ministan ya ce har yanzu kofa a bude take ga 'yan bindigan da za su mika wuya kuma su sake shiga cikin jama'a domin zaman lumana.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun sanar min salon da suke bi wurin guje wa luguden sojin sama, Gumi

Gwamnatin Buhari: Ba zamu iya kin yafewa 'yan bindiga, su ma 'yan Najeriya ne
Muhammad Dingyadi, Ministan 'Yan Sanda | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Ya kara da cewa 'yan bindigan da suka tuba su ma 'yan Najeriya ne kuma Gwamnatin Tarayya tana da alhakin sake hade su "cikin lumana da mutunci cikin al'umma".

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ministan ya ce:

“Tabbas, su masu laifi ne, sun aikata ta’asa, sun aikata laifuka, amma bisa ga dokokin duniya, lokacin da kuka mika wuya daga fagen yaki, ba a kashe ku, ba a cutar da ku, ana ba ku damar yin magana. .
"Muna sauraron su don ganin yadda za mu iya mai dasu cikin al'umma."

Da yake magana kan hare-haren da ake kaiwa ‘yan bindiga a Arewa maso Yamma, musamman Katsina, Zamfara da Sakkwato, Dingyadi ya ce gwamnati za ta ci gaba da yin nasarori muddin akwai hadin kai tsakanin hukumomin tsaro.

“Za ku ga karin nasarorin da ke tafe cikin kwanaki biyu masu zuwa. Jami'an tsaro suna aiki tukuru kan sahihancin iliminsu da kwarewar kayan aikinsu don samun gagarumar nasara akan maharan."

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

A tura 'yan Boko Haram da suka tuba zuwa gonaki, tsohon Janar ya shawarci FG

Tsohon shugaban horaswa da ayyuka a Hedikwatar rundunar Soji da ke Abuja, Birgediya Janar John Sura (mai ritaya), a ranar Juma'a, ya shawarci Gwamnatin Tarayya da ta tura 'yan ta'addan Boko Haram sama da 1,000 da suka tuba zuwa gona.

A cewarsa, ya kamata a yi amfani da su wajen aikin gona da suka hana ‘yan gudun hijira da sauran ‘yan Najeriya yi.

Ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa mai taken 'Ku dauki 'yan ta'addan Boko Haram da suka tuba a matsayin fursunonin yaki', jaridar Punch ta ruwaito.

Sura, wanda ya bayyana 'yan ta'addan da suka tuba a matsayin fursunonin yaki, ya bayar da hujjar cewa ya kamata a yi gyara ga Yarjejeniyar Geneva wacce ta ba su wasu gata kamar kariya daga duk wani aiki na tashin hankali gami da tsoratarwa, cin mutunci da sauransu.

Kara karanta wannan

Mun yi ta yi wa Buhari addu’o'i amma ba mu ga sakamako ba, inji Sheikh Khalid

a jaddada cewa ya kamata a kula da su a matsayin mutanen da ke zaman gidan yari kuma a sanya su cikin yanayin da ke ƙasa da na ‘yan sansanin gudun hijira.

Shugabannin Boko Haram matsorata ne: Tubabben kwamandansu ya tona asiri

A wani labarin, Wani tsohon kwamandan ‘yan ta’addan Boko Haram, Adamu Rugurugu, ya ce ya yi watsi da ta’addanci ne sakamakon gano cewa akidar 'yan ta’addan Boko Haram zamba ce.

A cikin bidiyon da PRNigeria ta samu, kasurgumin dan ta'addan ya ce manyan shugabannin kungiyar a koyaushe za su aika su a kashe su ne a fagen daga, tare da yaudarar su cewa aljanna ce za ta zama makomar su idan an kashe su.

A cewar Mista Rugurugu, manyan shugabannin Boko Haram ba sa iya tunkarar sojoji sai dai buya daga baya suna amfani da mayakansu wajen kai hare-haren kan sojoji a arewa maso gabas.

Kara karanta wannan

Kai Ɗan Kanzagi Ne, Muƙunshin Gishiri Ka Fi Gishiri Zaƙi, Gumi Ya Yi Wa Kakakin Buhari Wankin Babban Bargo

Asali: Legit.ng

Online view pixel