'Yan bindiga sun sanar min salon da suke bi wurin guje wa luguden sojin sama, Gumi

'Yan bindiga sun sanar min salon da suke bi wurin guje wa luguden sojin sama, Gumi

  • Kamar yadda Sheikh Ahmad Gumi ya sanar, 'yan bindiga sun tabbatar da cewa luguden wuta ta jiragen yaki ba zai yi tasiri a kansu ba
  • Gumi ya ce 'yan fashin dajin sun san hanyoyinsu da kuma salon gujewa luguden ruwan wutan da sojin sama ke musu a dajika
  • Fitaccen malamin da ke shan caccaka, ya shawarci 'yan sanda da sauran jami'an tsaron kan dole ne su hada kai da makiyayan yankunan

Kaduna - Sanannen malamin addinin Islama mazaunin Kaduna, ya kara tabbatar wa da jama'a cewa a koda yasuhe ya na samun damar tattaunawa da 'yan fashin dajin da suka addabi arewacin Najeriya.

A takardar da malamin ya fitar a cikin kwanakin nan, ya bayyana cewa gungun 'yan bindiga sun sanar da shi cewa luguden ruwan wutan da sojin saman ke yi ba ya taba su, sai dai ya taba matansu da 'ya'yansu, domin kuwa suna da salon kauce musu, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Binciko Gaskiya: Da gaske ne DSS sun kama telan Buhari da ya yi masa dinkin Imo?

'Yan bindiga sun sanar min salon da suke bi wurin guje wa luguden sojin sama, Gumi
'Yan bindiga sun sanar min salon da suke bi wurin guje wa luguden sojin sama, Gumi. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Gumi ya ce 'yan bindigan sun kware tare da zama 'yan hannu wurin kauce wa duk wani bam da sojin sama za su wurgo, hakan ne yasa da kyar a iya kama su ko halaka su.

A wata takarda da TheCable ta gani, ya bayyana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Abinda ba dole ku sani ba shi ne, 'yan bindigan sun kirkiro hanyoyin tsere wa luguden wuta ta sama. Sun sanar da mu cewa, za ku iya kashe matansu da 'ya'yansu ne kawai ta wannan harin.
"Abin nufi shi ne, idan aka matsanta musu a Zamfara, babu shakka za su sauya wuraren zama. Toh dukkan Najeriya ce za ta kasance a wannan halin?

Wurin karin bayani, fitaccen malamin ya bayyana cewa bayanai masu kyau, tsarin jami'ai nagari da kuma hada kai da makiyaya, sasanci duk suna cikin hanyoyin shawo kan matsalar 'yan fashin daji.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Gumi ya yi hasashe mai ban mamaki, ya ce wasu 'yan siyasa sun fi 'yan bindiga ta’asa

Gumi ya kara da cewa:

"A zancen gaskiya, shari'a ce ke kare hakkokin jama'a. Kudi da lokaci da aka yi amfani da su da kyau babu shakka za su kashe cutar kuma zai gyara kasar nan, ya cire mata cutar ta'addanci da gurbatattun shugabanni."

Safarar makamai a Zamfara: Dubu 20 ake biya na AK-47, dubu 5 na harsasai

A wani labari na daban, Murtala Rufa'i malami ne jami'ar Usmanu Danfodiyo da ke Sokoto, ya ce wani binciken da yayi kan ta'addanci a Zamfara ya bayyana yadda jama'a ke samun kudi daga safarar makamai.

A rahotonsa mai take, "Ni dan bindiga ne": Binciken shekaru 10 kan 'yan fashin daji a jihar Zamfara, Rufai ya ce binciken ya nuna cewa akwai sama da makamai 60,000 a arewa maso yamma, The Cable ta wallafa.

Ya ce kamar makamai kamar bindigogin harbi jirgin sama, abun harba gurneti, AK-47, AK-49, da sauransu duk ana samun su a sansanonin 'yan bindiga a jihar.

Kara karanta wannan

Ni Soja ne, Likita kuma Malami mai Digiri 3, saboda haka ba zan yi shiru ba: Sheikh Gumi

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng