Yadda dakile layin wayoyin GSM ya jawo ‘Yan bindiga suka kai wa Sojoji hari a Zamfara

Yadda dakile layin wayoyin GSM ya jawo ‘Yan bindiga suka kai wa Sojoji hari a Zamfara

  • ‘Yan bindiga sun shiga sansanin jami’an tsaro a jihar Zamfara, sun yi barna
  • Hakan ya yiwu ne saboda kashe hanyoyin sadarwan da hukumar NCC ta yi
  • Duk da hakan ya taimaka, rashin sadarwan ya jawo wa jami’an tsaro cikas

ZamfaraDaily Trust tace harin da aka kai wa dakarun jami’an tsaro a jihar Zamfara a ranar Asabar ya yiwu ne saboda kashe hanyoyin sadarwa da aka yi.

‘Yan bindiga sun shiga sansanin runduna da ke Mutumji, suka kashe sojojin ruwa tara, sojan kasa daya da wani jami’in ‘dan sanda, sannan suka saci makamai.

Rahoton yace abin da ya faru shi ne miyagun sun yi amfani da damar rashin sadarwa, suka kai harin.

Sojoji ba su da hanyar yin waya

Wata majiya ta shaida wa manema labarai cewa mafi yawan sojoji suna amfani da wayoyin salula ne wajen sadarwa, manyan soji ke amfani da wayar oba-oba.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Mutane da Dama Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga Daga Zamfara Suka Faɗa Sansanin Sojoji Cikin Rashin Sani

“Ko da toshe layukan wayoyin salula ya taimaka wajen dakile ‘yan bindiga a Zamfara, hakan kuma ya kawo wa sojoji cikas domin babu wata kafar sadarwa.”

Sojoji a bakin aiki
Dakarun sojojin Najeriya Hoto: www.voanews.com
Asali: UGC

“Manyan dakarun sojoji ke amfani da rediyon soja ko salular walkie-talkie, a dalilin haka, jami’an tsaro da ke fagen yaki suna aiki ne da wayoyin salularsu.”
“Yan bindiga sun yi amfani da wannan dama, suka kai masu hari a sansaninsu. Akwai bukatar sojoji su tanadi samu na’urorin sadarwa na musamman.”

Har yau wasu ‘yan bindiga suna iya yin waya ta hanyar amfani da wayoyi irinsu Thuraya ko aiki da layin Airtel da Glo ko kuma su shiga yankunan Sokoto da Kaduna.

NSA bai sa hannu ba

Wata majiyar tace Gwamna Bello Matawalle ne ya tuntubi Dr. Isa Ali Pantami a kan batun, shi kuma ya zauna da shugaban kasa Muhammadu Buhari kai-tsaye.

Kara karanta wannan

A karshe ma’aikatan gonar Obasanjo sun samu ‘yanci bayan kwana 3 a ramin masu garkuwa da mutane

Fadar shugaban kasa ta bada izinin rufe kafofin sadarwa a Zamfara ba tare da amincewar ofishin mai bada shawara kan harkar tsaro ba, wanda hakan yana da illa.

An kashe mutane a Kaduna

Jiya Gwamnatin Kaduna ta tabbatar da mutuwar mutane 12 a harin Zangon Kataf. Samuel Aruwan ya fitar da jawabi, yace za a binciki wadanda suka kai harin.

Ba wannan ne karon farko da aka hallaka mutane a yankin kudancin Kaduna ba. Gwamna Nasir El-Rufai ya mika ta'aziyyarsa ga iyalan wadanda suka rasu a harin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel