Ba tsaro a Najeriya, sai zubar da jini ake, inji Sule Lamido yayin ganawa da Obasanjo
- Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya ziyarci tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo
- Ya bayyana cewa, Najeriya na cikin wani hali, babu wani wanda ke cikin kwanciyar hankali
- Obasanjo a wani bangaren, ya bayyana cewa zai yi komai domin Najeriya ta magance kalubalenta
Abeokuta, Ogun - Sule Lamido, tsohon gwamnan Jigawa, ya ce Najeriya na zubar da jini domin babu inda ba a fuskantar rashin tsaro a kasar, TheCable ta ruwaito.
Jigon na jam’iyyar adawa ta PDP ya bayyana hakan ne a karshen mako bayan ganawa da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo a gidansa da ke Abeokuta, jihar Ogun.
Kamar yadda wata sanarwa da Kehinde Akinyemi, mai magana da yawun tsohon shugaban kasar ya fitar ranar Lahadi 12 ga watan Satumba, Lamido ya ce duk da Najeriya na fuskantar kalubale, ganawarsa da Obasanjo ya karfafa imaninsa a kasar.
A cewarsa:
"Ta yaya za mu ci gaba da zama lafiya? Ita ce babbar matsala da kalubale a yanzu a cikin wannan kasar, saboda yanzu, babu wanda ya ke zaune lafiya kuma.
“Ku yi tunanin! Sace ma'aikatan Baba uku, tsohon Shugaban kasa. Wanene ya ke zaune lafiya? ”
A cewar sanarwar, Lamido ya ce ya ziyarci Obasanjo a matsayin "uba kuma jagora da komai na" bayan dogon lokaci, ya kara da cewa ya sadu da tsohon shugaban "cikin matukar kwarin gwiwa da koshin lafiya".
Sule Lamido ya bayyana irin tattaunawar kwarin gwiwar da ya samu daga tsohon shugaban kasar, inda Obasanjo ya bayyana cewa, zai yi komai don tabbatar da tsayuwar Najeriya.
Mun yi ta yi wa Buhari addu’o'i amma ba mu ga sakamako ba, inji Sheikh Khalid
Babban limamin masallacin Juma’a na Apo Legislative Quarters dake Abuja, Sheikh Muhammad Khalid, kwanan nan ya yi fice a kafafen sada zumunta bayan faifan bidiyon wa’azin sa da ya soki shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya bazu.
A cikin wata hirar da Legit.ng Hausa ta samo daga jaridar Punch, malamin addinin Islaman ya ce yana tsaye kan kalamansa cewa shugaban bai tsinana komai ba.
A tattaunawar, malamin ya bayyana abubuwan da suke damunsa game da gwamnatin shugaba Buhari, wadanda a cewarsa gwamnatin ta cika yiwa 'yan Najeriya karerayi.
A bangare guda, ya kuma bayyana cewa, addininsa ya horar da shi da fadin gaskiya da adalci, don haka dole ne ya fadi gaskiya game yadda mulkin Buhari yake kamar yadda ya yi a lokacin Jonathan.
Na kudiri aniyar gurfanar da 'yan ta'adda a gaban kuliya, inji Buhari
A wani labarin, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce gwamnatinsa ta kuduri aniyar cafke mutanen da ke da hannu a kashe-kashen da aka yi a jihar Filato, inji rahoton TheCable.
A cikin watanni uku da suka gabata, hare-hare a sassa daban-daban na jihar sun yi sanadiyar mutuwar mutane sama da dari.
Buhari, wanda Boss Mustapha, sakataren gwamnatin tarayya (SGF) ya wakilta, a wani zaman tattaunawa tare da masu ruwa da tsaki a jihar a ranar Litinin 6 ga watan Satumba, ya bukaci tattaunawa mai dorewa don samar da zaman lafiya a Filato.
Asali: Legit.ng