Jerin gwamnonin Najeriya na yanzu da za su iya rasa zaben 2023 da dalili

Jerin gwamnonin Najeriya na yanzu da za su iya rasa zaben 2023 da dalili

  • A ka'idar siyasar Najeriya, shugaban kasa da gwamnoni kan yi shekaru takwas ne kacal a kan karagar mulki
  • Duba ga wannan al'ada ta siyasar kasar, kimanin gwamnoni 18 masu ci a yanzu ne za su hakura da wannan kujera domin za su kammala wa'adinsu na biyu a 2023
  • Tsohon shugaban kasa Obasanjo ya so zarcewa a wa'adi na uku a lokacin mulkinsa amma mutane suka yi adawa da hakan

Tarayyar Najeriya - Ga dukkan alamu akwai yarjejeniya a fagen siyasar Najeriya cewa babu wani shugaba ko gwamna da zai iya yin tazarce a karo na uku duk da cewar ba a fayyace wannan a cikin kundin tsarin mulkin kasar ba.

Wannan al’ada tayi aiki sosai ne a ƙarshen gwamnatin tsohon shugaban ƙasa Olusegun Obasanjo a 2007 lokacin da aka yi ikirarin cewa zai sake yin wani wa'adin (bayan ya shae shekaru takwas a karagar mulki) inda aka yi adawa da hakan kamar yadda yake a wallafar Vanguard.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan kudu maso gabas ya ce ya yi wuri da za a fara zancen shugabancin Ibo, ya ba da dalili

Jerin gwamnonin Najeriya na yanzu da za su iya rasa zaben 2023 da dalili
Jerin gwamnonin Najeriya na yanzu da za su iya rasa zaben 2023 da dalili Hoto: Nigerian Senate
Asali: Facebook

Wannan na tabbatar da cewa yawancin gwamnoni masu ci a yanzu da suka riga suka hau kujerar mulki a karo na biyu ba za su iya shiga babban zaben da ake sa ran za a yi a 2023 ba.

Legit.ng ta kawo cikakken jerin sunayen irin wadannan gwamnoni:

1. Gwamna Okezie Ikpeazu (Abia)

2. Gwamna Udom Gabriel Emmannuel (Akwa Ibom)

3. Gwamna Willie Obiano (Anambra)

4. Gwamna Samuel Ortom (Benue)

5. Gwamna Benedict Ayade (Cross River)

6. Gwamna Ifeanyi Okowa (Delta)

7. Gwamna Ifeanyi Ugwuanyi (Enugu)

8. Gwamna Badaru Abubakar (Jigawa)

9. Gwamna Abdullahi Ganduje (Kano)

10. Gwamna Aminu Masari (Katsina)

11. Gwamna Abubakar Atiku Bagudu (Kebbi)

12. Gwamna Abubakar Sani Bello (Neja)

Kara karanta wannan

Babban taro: Majiyoyin PDP sun ce tsofaffin gwamnoni na iya samar da shugaban jam’iyyar na kasa na gaba

13. Gwamna Simon Lalong (Filato)

14. Gwamna Nyesom Wike (Ribas)

15. Gwamna Aminu Waziri Tambuwal (Sokoto)

16. Gwamna Darius Ishaku (Taraba)

17. Gwamna Dave Umahi (Ebonyi)

18. Gwamna Nasir El-Rufai (Kaduna)

Gwamnonin PDP: Zamu Haɗa Kan Mu Domin Ceto Najeriya Daga Hannun Jam'iyyar APC a Zaben 2023

A wani labarin. gwamnonin PDP sun bayyana cewa zasu haɗa kan jam'iyyar su domin ceto Najeriya daga hannun gurbatacciyar gwamnatin APC a zaben 2023.

Shugaban kungiyar gwamnonin kuma gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal, shine ya bayyana haka ga manema labarai ranar Laraba da daddare, jim kaɗan bayan taron da suka gudanar a Abuja.

Yace taron wanda ya gudana a sirrince sun cimma nasara, inda suka tattauna kan gangamin taron PDP na ƙasa dake tafe.

Asali: Legit.ng

Online view pixel