Kwankwaso ya yi kunnen uwar-shegu da gayyatar EFCC, akwai yiwuwar a yi ram da shi

Kwankwaso ya yi kunnen uwar-shegu da gayyatar EFCC, akwai yiwuwar a yi ram da shi

  • Majiya daga hukumar EFCC ta ce ana iya kama Kwankwaso idan bai amsa gayyatar hukumar ba
  • Hukumar yaki da rashawar ta gayyaci Kwankwaso ne bisa korafin da aka kai kansa na zargin aikata ba dai-dai ba
  • Kungiyar Ma'aikatan Kano da Yan Fansho ne suka yi korafin kan Kwankwaso na zarginsa da karkatar da kudade na gina gidajen ma'aikata da rabawa na kusa da shi gidaje

FCT Abuja - Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso ya ki amsa gayyatar hukumar yaki da rashawa ta EFCC, a makon da ta gabata kamar yadda Premium Times ta ruwaito.

An gayyaci dan siyasan ne domin ya amsa tambayoyi da suka shafi zargin amfani da ofishinsa ba ta yadda ya dace ba, karkatar da kudaden al'umma da bawa wasu na kusa da shi gidaje ba bisa ka'ida ba.

Kara karanta wannan

Bidiyon katon din giya 3,600 da Hisbah ta kama an ɓoye cikin buhunan abincin kaji a Kano

Akwai yiwuwar a kama Kwankwaso idan ya ƙi amsa gayyatar hukumar EFCC, Majiya
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso. Hoto: Premium Times
Asali: Depositphotos

Majiyoyi sun ce an bukaci Kwankwaso, jigo a jam'iyyar PDP ya bayyana a hedkwatar EFCC a ranar Alhamis da ta gabata a Abuja amma ya ki amsa gayyatar.

Kwankwaso bai amsa sakon kar ta kwana ba da aka aika masa domin jin ta bakinsa game da lamarin. Bai kuma daga wayarsa ba.

Premium Times ta ruwaito cewa majiyoyi daga hukumar EFCC sun ce ana iya kama Kwankwaso idan har ya cigaba da kin amsa gayyatar da hukumar ke masa na zuwa ya amsa tambayoyi.

Dalilin gayyatar Kwankwaso?

Sanadin binciken shine wani takardan korafi da kungiyar 'yan fansho da ma'aikatan jihar Kano suka shigar a 2015, inda suka yi ikirarin Kwankwaso ya sabawa dokar Garatuti ta 2007 yayin rike kudin fansho da ya kai Naira biliyan 10 daga 2011 zuwa 2015.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: ‘Yan bindiga sun kai farmaki gidan yari, sun saki fursunoni 240 sannan suka kashe sojoji a Kogi

Kwankwaso ya yi gwamna a Kano tsakanin 2011 zuwa 2015. A baya, ya rike mukamin daga 1999 zuwa 2003.

A cewar masu korafin, Kwankwaso ya bada umurnin a yi amfani da kudin fanshon wurin gina gidaje da ya kamata mafi yawancin yan fanshon su amfana da su. An cimma yarjejeniya tsakanin hukumar fansho ta Kano, a matsayin masu saka jari, yayin da gwamnatin Kano da Hukumar Gidaje na Kano za su yi aikin a kasafi na 60:40.

Sai dai bayan bada kwangilan gina gidaje 1,579 a 'biranen Kwankwasiya, Amana da Bandarawa' masu karar sun yi ikirarin Kwakwaso ya saba wasu alkawuran da aka yi ya rika bawa wasu na kusa da shi gidaje.

Sun yi zargin lamarin ya faru ne a Mayun 2015, watan da Kwankwaso ya bar ofis a matsayin gwamna.

2023: Ba mu buƙatar Atiku ya sake takara, Ya tafi Dubai ya manta da mu tunda ya sha kaye a 2019, Ƙungiyar PDP

Kara karanta wannan

Obaseki: Babban tashin hankali na bayan na bar kujerar gwamna

A wani labarin daban, wata kungiya mai suna People’s Democratic Party (PDP) Action 2023, ta bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kada ya sake takara a shekarar 2023 don ya yi watsi da jam'iyyar ya koma Dubai, UAE, tunda ya fadi zabe a 2019, rahoton Daily Trust.

Atiku, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, bai riga ya bayyana niyarsa na son sake takara ba a 2023, amma, dansa, Adamu Atiku Abubakar, ya tabbatar cewa zai sake takara.

Amma a martaninsa, Atikun ya ce ba watsi da jam'iyyar ta PDP ya yi ba, ya tafi yin karatun digiri na biyu ne a kasar waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164