Obaseki: Babban tashin hankali na bayan na bar kujerar gwamna

Obaseki: Babban tashin hankali na bayan na bar kujerar gwamna

  • Gwamnan jihar Edo, Godwin Obaseki, ya ce akwai babban abinda ya ke tsoro idan ya bar kujerar gwamnan jihar
  • Obaseki ya ce ya kawo sauye-sauye a fannin ilimi da manyan ma'aikatun jihar a cikin shekaru 5 da suka gabata kuma zai cigaba har 2024
  • Kalubalen da ya ke tsoro shi ne mene ne makomar gyare-gyaren da yayi wa jihar bayan ya kammala wa'adin mulkinsa nan da shekaru 3

Edo - Gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo a ranar Lahadi ya yi magana kan babban tashin hankalinsa da tsoro bayan ya bar kujerar gwamna.

Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, gwamnan da zai kammala mulkinsa karo na biyu a 2024, ya ce babban kalubalensa shi ne abinda zai faru da gyare-gyarensa nan da shekaru uku masu zuwa.

Kara karanta wannan

2023: Gwamnan kudu maso gabas ya ce ya yi wuri da za a fara zancen shugabancin Ibo, ya ba da dalili

Obaseki: Babban tashin hankali na bayan na bar kujerar gwamna
Gwamna Obaseki ya ce babban tsoronsa shi ne abinda zai faru da gyaregyaren da zai yi nan da shekaru uku. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Ya sanar da hakan ne a Benin, babban birnin jihar Edo yayin addu'ar ciki shekaru 87 ta Chief Gabriel Igbinedion da aka shirya a coci.

Obaseki ya ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Muna ta karfafawa da kuma kara gina ingantaccen ilimi a fadin jihar nan wanda ya hada na firamare, sakandare da na jami'a tare da saka hannayen jari a shekaru 5 da suka gabata.
"A bangaren yada labarai kuwa, muna cigaba da kokarin gina na kanmu tunda muna da kafar yada labari ta Edo da kuma talabijin din mu.
"Muna kokarin samar musu da kayan aiki na zamani wadanda suka cika na fasaha.
"Amma babban kalubale na shi ne abinda zai faru bayan na bar kujerar. Jama'a na cewa, wanne tabbacin garemu na cewa gyara da sauyin da muka kawo za su cigaba da wanzuwa bayan na bar ofishin?"

Kara karanta wannan

Zamfara: Gwamnati ta kwace kayan abinci da man fetur da aka yi yunkurin kai wa 'yan fashin daji

Ya ce abu mai tabbaci shi ne su cigaba da karfafawa tare da gina bangarorin gwamnati kafin a kawo 'yan siyasa su shiga lamarin kafin zuwan lokacin.

Ya ce:

"Akwai tabbacin cewa tsarin da muke cigaba da dasawa babu shakka za su cigaba da wanzuwa."

Ya ce gwamnatin jihar ta dauka ma'aikata 300 inda ya kara da cewa sai ya dauka ma'aikata 2,000 a cikin shekaru 3 masu zuwa domin karfafa ayyukan gwamnati, Daily Trust ta ruwaito.

Ya ce kwamishinonin jihar ba za su iya yin komai ba matukar ma'aikatan gwamnatin ba su iya aikin da ya dace.

NAPTIP: Rashin jituwa da Minista Sadiya Faruk ya sa aka fatattaki tsohon sanata

A wani labari na daban, Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sallami Sanata Basheer Mohammed, darakta janar na hukumar yaki da safarar jama'a (NAPTIP).

Daily Trust ta ruwaito cewa, an sallami Mohammed kasa da watanni hudu da ya karbi ragamar hukumar.

Kara karanta wannan

Labari Mai Daɗi: Jihar Kogi Za Ta Fara Samar da Man Fetur, Yahaya Bello

Shehu ya ce an yi nadin ne sakamakon bukatar ministan walwala da jin kan 'yan kasa, Hajiya Sadiya Umar Farouk, Daily Trust ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

Tags: