2023: Ba mu buƙatar Atiku ya sake takara, Ya tafi Dubai ya manta da mu tunda ya sha kaye a 2019, Ƙungiyar PDP
- Wata kungiya ta jam'iyyar PDP ta bukaci Atiku Abubakar ya hakura da fitowa takara a 2023
- Kungiyar mai suna People’s Democratic Party (PDP) Action 2023 ta zargi Atiku da watsi da jam'iyyar bayan ya fadi zaben 2019
- A cewar kungiyar Atiku ya koma ya tare a Dubai, sai yanzu ne da zabe ke karatowa ya dawo, ta ce ya bawa matashi dama ya yi takarar
FCT, Abuja - Wata kungiya mai suna People’s Democratic Party (PDP) Action 2023, ta bukaci tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar kada ya sake takara a shekarar 2023 don ya yi watsi da jam'iyyar ya koma Dubai, UAE, tunda ya fadi zabe a 2019, rahoton Daily Trust.
Atiku, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a zaben 2019, bai riga ya bayyana niyarsa na son sake takara ba a 2023, amma, dansa, Adamu Atiku Abubakar, ya tabbatar cewa zai sake takara.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Laraba a Abuja, shugaban kungiyar Hon. Rufus Omeire, ya ce:
"Cin amana ne yadda Atiku Abubakar ya yi watsi da mutane da masu zabe da suka mara masa baya tare da yin sadaukarwa a PDP a shekarar 2019.
"Yanzu da zaben 2023 ke karatowa, ya dawo ya fara kokarin motsi na siyasa kuma. Bisa dukkan alamu, abin da kadai ya iya sosai a rayuwarsa shine siyasa.
"Muna tunanin lokaci ya yi da Alhaji Atiku Abubakar, GCON, zai koma gefe ya kyalle wasu su yi takara, idan so samu dan takara mai kananan shekaru ya fito ya yi takara."
Ba a samu ji ta bakin hadimin Atiku ba
Rahoton na Daily Trust ya ce, Paul Ibe, mashawarcin na musamman kan siyasa na Atiku bai amsa kirar ba da sakon kar ta kwana da WhatsApp da aka aike masa yayin hada wannan rahoton.
2023: APC na fuskantar sabuwar barazana yayin da Atiku da Obaseki suka hadu kan yadda PDP za ta kada jam'iyyar
Ka Ji Kunya: Sadaukin Shinkafi ya soki Mataimakin Gwamnan Zamfara kan ƙin sauya sheƙa zuwa APC
Tsohon ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode (Sadaukin Shinkafi) ya yi wa Mataimakin Gwamnan jihar Zamfara, Mahdi Gusau, wankin babban bargo a kan kin komawa jam’iyyar APC.
A wata wallafa da Tsohon ministan yayi ta shafinsa na Twitter, wanda shi din jigo ne na jam’iyyar PDP, ya ce Mahdi bai nuna da’a ba ga gwamnansa, Bello Matawalle, wanda ya canja sheka daga PDP zuwa APC, premium times ta ruwaito.
Gwamnan jihar Zamfara tare da ‘yan majalisar jihar da sauran kwamishinonin jihar sun koma jam’iyyar APC a watan Yuli, bayan watanni kadan da gwamna Ben Ayade na jihar Cross River da David Umahi na jihar Ebonyi suka koma jam’iyya mai mulkin.
Asali: Legit.ng