Mataimakin Gwamna Ya Yi Magana Kan Shirinsa Na Ficewa Daga Jam'iyyar PDP
- Mataimakin gwamnan Edo, Philip Shaibu, ya bayyana cewa babu wata matsala tsakaninsa da uban gidansa, Gwamna Obaseki
- Shaibu ya faɗi cewa tabbas akwai matsalolin dake faruwa a cikin PDP, amma bai shafi alakarsa da gwamna ba
- Kakakin mataimakin gwamnan, Musa, yace jita-jitar shirin ficewar uban gidansa daga PDP ba gaskiya ba ce
Edo - Mataimakin gwamnan jihar Edo, Philip Shaibu, ya musanta jita-jitar raba gari da uban gidansa, Gwamna Godwin Obaseki, kamar yadda leadership ta ruwaito.
Mataimakin gwamnan ya faɗi haka ne yayin da ya bayyana a cikin shirin Channels tv na 'Politics Today' ranar Litinin.
Mista Shaibu ya yi watsi da duk wani rahoton cewa basa ga maciji tsakaninsa da gwamna, ya kuma jaddada goyon bayansa ga uban gidansa.
Mataimakin gwamnan yace:
"Ina farin ciki da alakar dake tsakanina da gwamna, babu wata matsala a tsakanin mu."
"Bansan inda aka zaƙulo maganar mun samu matsala da mai girma gwamna ba, har yanzun ina goyon bayansa."
Wace matsala ke faruwa a cikin PDP?
Sai dai mataimakin gwamnan ya amsa wata tambaya da cewa akwai abubuwan dake wakana a cikin jam'iyyar PDP mai mulkin jihar.
"Eh tabbas akwai abubuwa mara dadi dake wakana a cikin jam'iyyar PDP, wanda muke kokarin warwarewa."
Shin dagaske ne zai fice daga PDP?
A jawabin mista Shaibu, bai bayyana kai tsaye cewa dagaske ne ya gama shirin ficewa daga PDP ko kuma ba gaskiya bane.
Legit.ng Hausa ta gano cewa mataimakin gwamnan ya yi wannan zancen ne a dai-dai lokacin da ake yaɗa jita-jitar cewa ya gama shirin ficewa daga PDP zuwa wata jam'iyya saboda rikicin PDP.
Sai dai mai magana da yawun mataimakin gwamnan, Ebomhiana Musa, ya musanta rahoton da cewa duk soki burutsu ne.
Ba zan sake afuwa gare ku ba, gwamnan arewa ga ‘yan bindiga, ya sha alwashin hukunta masu daukar nauyinsu
A cewar Musa, maganar dake yawo cewa Shaibu ya kammala shirin fita daga PDP tsantsagoron karya ce da aka kirkira.
A wani labarin kuma Jam'iyyar APC mai mulki ta sanar da ranar gangamin taronta na Jihohi
Jam'iyyar APC ta kasa ta bayyana ranar 2 ga watan Oktoba a matsayin ranar da zata gudanar da gangamin tarukanta na jihohi.
Jam'iyyar ta kuma sanar da cewa zata fara siyar da fom ɗin takara yayin taron, wanda za'a zaɓi shugabannin jihohi, ranar 15 ga watan Satumba.
Asali: Legit.ng