Da Ɗuminsa: Mataimakin Gwamna Ya Raba Gari da Gwamna, Zai Fice Daga Jam'iyyar PDP

Da Ɗuminsa: Mataimakin Gwamna Ya Raba Gari da Gwamna, Zai Fice Daga Jam'iyyar PDP

  • Manyan alamu sun nuna cewa mataimakin gwamnan Edo, Philip Shaibu, zai fice daga jam'iyyar PDP
  • Rahoto ya nuna cewa mataimakin gwamnan ya gudanar da wasu taruka da kusoshin siyasa yayin hutunsa a ƙasar waje
  • Gabanin zaɓen jihar na 2020, gwamna Obaseki da mataimakinsa suka jagoranci ɗumbin magoya baya zuwa PDP daga APC

Edo - Mataimakin gwamnan jihar Edo, Mr. Philip Shaibu, yana shirin ficewa daga jam'iyyar PDP zuwa wata jam'iyya da ba'a bayyana ba.

Vanguard ta rahoto cewa matukar jerin taron da mataimakin gwamnan yake gudanarwa tare da wasu kusoshin siyasa a jihar yana da alaƙa da shirinsa, to yana iya bayyana ficewarsa kowane lokaci daga yanzu.

Rahotanni sun bayyana cewa mataimakin gwamnan ya ɗauki hutu, kuma ya yi amfani da wannan lokacin wajen tattaunawa kan lamarin kafin dawowarsa Najeriya a makon da ya gabata.

Kara karanta wannan

Ba zan sake afuwa gare ku ba, gwamnan arewa ga ‘yan bindiga, ya sha alwashin hukunta masu daukar nauyinsu

Philip Shaibu
Da Ɗuminsa: Mataimakin Gwamna Ya Raba Gari da Gwamna, Zai Fice Daga Jam'iyyar PDP Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Wace jam'iyya mataimakin gwamnan zai koma?

Wani majiya da ya nemi a sirrinta shi, ya bayyana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Philip Shaibu, mutum ne da nake kauna a siyasar jihar Edo, ficewarsa daga PDP zai jawo babban naƙasu ga kokakrin kawo cigaba da gwamnatin Obaseki take yi."

A cewar mutumin, akwai alamu masu ƙarfi dake nuna cewa babu wata jam'iyya da mataimakin gwamnan zai koma da zaran ya fice daga PDP.

Duk wani kokari na jin ta bakin babban mai taimakawa mataimakin gwamnan ta ɓangaren yaɗa labarai, Benjamin Atu, domin ya yi magana kan jita-jitar da kuma bayyana ranar ficewar uban gidansa ya ci tura.

Gab da zaɓen 2020 suka sauya sheka

Gabanin zaɓen gwamna 2020, Gwamna Obaseki, da mataimakinsa, Philip Shaibu, suka jagoranci magoya bayansu zuwa jam'iyyar PDP.

Shu'aibu, wanda ya zanta da manema labarai bayan ya karbi katin zama ɗan PDP, ya nuna rashin jin daɗinsa da mulkim kama karya na shugaban APC, Adams Oshiomhole.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP: Zamu Haɗa Karfi da Karfe Domin Ceto Najeriya Daga Hannun Jam'iyyar APC a Zaben 2023

Wane mataki PDP ta ɗauka kan shirin Shuaibu?

Da aka tuntubi mataimakin kakakin jam'iyyar PDP na ƙasa, Duran Odeyemi, yace ba shi da labarin shirin sauya shekar mataimakin gwamnan.

A wani labarin kuma Mutane Sun Yi Asarar Miliyoyin Nairori Yayin da Wata Tankar Man Fetur Ta Kama da Wuta a Yola

Mutane sun yi asarar dukiya ta miliyoyin nairori da sanyin safiyar Litinin a wani lamarin gobara da ya auku a jihar Adamawa, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne yayin da wata tankar dakon man fetur, makare da man, ta kama da wuta bayan ta faɗi a shatale-talen Maidoki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel