Da Dumi-Duminsa: Jam'iyyar APC Ta Sanar da Ranar Gangamin Taronta na Jihohi
- Jam'iyyar APC ta kasa ta bayyana ranar 2 ga watan Oktoba a matsayin ranar da zata gudanar da gangamin tarukanta na jihohi
- Jam'iyyar ta kuma sanar da cewa zata fara siyar da fom ɗin takara yayin taron, wanda za'a zaɓi shugabannin jihohi, ranar 15 ga watan Satumba
- A baya APC ta gudanar da zaɓukanta a matakin gundumomi da kuma ƙananan hukumomi dake faɗin kasar nan
Abuja - Kwamitin rikon kwarya na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) ya bayyana ranar da za'a gudanar da tarukan jam'iyya a matakin jihohi, kamar yadda the nation ta ruwaito.
Kwamitin ya sanar da cewa za'a gudanar da gangamin tarukan APC a matakin jihohi ranar Asabar, 2 ga watan Oktoba, inda za'a zabi shugabannin APC a jihohi.
Wannan na kunshe ne a wani gajeren jawabi da sakataren kwamitin rikon kwarya na APC ta kasa, Sanata John James Akpanudoedehe, ya fitar ranar Litinin a Abuja.
Yaushe za'a fara siyar da fom ɗin takara?
Bugu da kari, sakataren ya sanar da cewa jam'iyyar zata fara siyar da fom na gangamin tarukan daga ranar Laraba, 15 ga watan Satumba, 2021.
Legit.ng Hausa ta rahoto muku cewa APC ta fara gudanar da tarukanta ne daga matakin gundumomi, inda aka gudanar da zaɓen shugabannin APC a matakin.
Tarukan APC na gundumomi ya gudana ne ranar 31 ga watan Yuli 2021, yayin da na kananan hukumomi ya gudana ranar 4 ga watan Satumba, kamar yadda channels tv ta ruwaito.
A wani labarin kuma Majlisar Dokoki Ta Dakatar da Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye
Majalisar dokokin jihar Nasarawa ta dakatar da mataimakin shugaban marasa rinjaye, Luka Zhekaba (PDP-Obi 2), bisa zarginsa da hannu a ɗaukar malaman sakandire ba bisa ƙa'ida ba a jihar.
Kakakin majalisar, Ibrahim Abdullahi, ya kafa kwamitin wucin gadi na mutum uku da zai binciki lamarin.
Asali: Legit.ng