Wata makaranta ta kori dalibai 8 saboda sunyi cikin shege

Wata makaranta ta kori dalibai 8 saboda sunyi cikin shege

Dalibai 8 ne yan makarantar Elgeyo Marakwet, Kenya aka kora lokacin da aka gano suna da ciki.

Wata makaranta ta kori dalibai 8 saboda sunyi cikin shege

Hukumar makarantar dai ta bayyana dalilin korar tasu da cewa hakan zai iya bata mata suna wanda su kuma sukace bazasu lamunta ba. Lokacin da iyayen daliban suke tsokaci game da lamarin, da yawa daga cikin su sun nuna rashin jin dadin su da hukuncin da makarantar ta dauka kan yaran nasu.

Haka kuma iyayen sun nuna rashin jin dadin nasu game da yadda sukace makarantar ta bata wa yaran su suna inda har ta kai ga yanzu ba inda a ke iya daukar yaran wata makaranta. Lokacin da suke zantawa da manema labarai, uban daya daga cikin yaran yace: "Mu dai bamu ji dadi ba don kuwa korar da akayi ma yaran namu ya sa an bata masu karatun su ya kuma illata ilimin yaran namu don ya maida su ba.

Abun na da matukar bacin rai ganin yadda muke sa ran yayan namu su zamu wani abu nan gaba amma ana neman a hana hakan yiwuwa." Daga bisani kuma sai suka bukaci gwamnati data shigo cikin lamarin domin ganowa tare da hukunta hatsabiban da suka yi ma yaran nasu ciki. Yanzu haka dai yaran an kai su asibiti suna ci gaba da renon cikin nasu kafin kammalar bincike.

Asali: Legit.ng

Online view pixel