Zamfara: 'Yan fashin daji sun fara bukatar taliya da shinkafa a maimakon kudin fansa

Zamfara: 'Yan fashin daji sun fara bukatar taliya da shinkafa a maimakon kudin fansa

  • 'Yan fashin daji a jihohin arewa maso yamma sun fara shiga mawuyacin hali tun bayan rufe kasuwanni
  • Sun fara bukatar buhunan shinkafa, kwalayen taliya da na ruwan lemo a madadin kudin fansar wadanda suka sace
  • Wasu mazauna yankin sun sanar da yadda yunwa ta gigita 'yan bindigan har suka karba mudu goma na shinkafa a matsayin fansa

Zamfara - Rufe kasuwanni masu yawa a fadin jihohin arewa maso yamma na Najeriya ya kasance babban kalubale ga 'yan fashin daji.

Daily Trust ta ruwaito cewa, a kalla gwamnonin yankin hudu ne suka umarci rufe kasuwannin jihohinsu a matsayin hanyar dakile ta'addanci.

Kwanaki kadan bayan rufe kasuwannin a wasu kayukan Sokoto, 'yan fashin daji sun fara bukatar kayan abinci a matsayin fansar wadanda ke hannunsu.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Jami'in dan sanda ya harbe abokin aikinsa dan sanda a jihar Kano

Zamfara: 'Yan fashin daji sun fara bukatar taliya da shinkafa a maimakon kudin fansa
Zamfara: 'Yan fashin daji sun fara bukatar taliya da shinkafa a maimakon kudin fansa. Hoto daga dailytrust.com
Asali: UGC

Wani mazaunin Sabon Birni, wanda ya bukaci a rufa sunan shi, ya sanar da Daily Trust yadda aka sako wata diyar makwabtansu bayan sun bada kayan abinci.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Sun sace diyar wani mutum a kauyenmu kuma ya kasa hada kudi, sai suka ce ya kai mudu goma na shinkafa a matsayin fansar diyarsa. Haka kuwa a ka yi."

Wani mazaunin Sokoto ya sanar da Daily Trust yadda 'yan bindiga suka bukaci kayan abinci da abubuwan sha domin sakin direban da suka sace.

Da farko sun bukaci kudin fansa har N15 miliyan, amma daga baya sun amince za su karba N600,000.

"Sun bukaci a yi amfani da kudin wurin siyan buhunan shinkafa, katon din abin sha, kwalin taliya, sigari da sauransu. Har yanzu dai ana tattaro kudin," yace.

Me masana suka ce?

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke wadanda suka kashe mahaifin tsohon gwamnan Filato

Wani masani a fannin tsaro, Aminu Bala Sokoto, ya ce halin da aka shiga ya nuna cewa tsanantawar da sojoji suka yi kan 'yan bindigan a Zamfara ya na haifar da nasarori.

"Ayyukan suna gurgunta su saboda ba su kadai ba, hatta rumbunansu suna shan wuya. A halin yanzu sun kidime, neman yadda za su rayu su ke yi.
“Al'amarin ya kara wahala tun bayan da aka datse hanyoyin sadarwa a Zamfara da Katsina saboda ba su iya samun 'yan uwan wadanda suka sace.
“Ina fatan wannan datsewan zai hada da sauran jihohin da ke yankin," yace.

Wadanda ake zargi sun sanar da dalilinsu na sacewa da sheke mahaifin tsohon gwamna

A wani labari na daban, makasan Pa Defwan Dariye, mahaifin tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye sun bayyana cewa sun yi garkuwa da shi ne don su samu kudade daga hannun dan sa.

Daily Trust ta ruwaito cewa, daya daga cikin wadanda ake zargin ya ce Jethro Nguyen mai shekaru 53 dan asalin Bakos da ke jihar Filato ne ya hallaka Dariye.

Kara karanta wannan

Sunday Igboho ya ce a mika shi ga Najeriya bai jin tsoron karo da gwamnatin Buhari

Daya daga cikin su mai suna Sunday Ibrahim, ya kara tabbatar da cewa Nguyen ne wanda ya shirya komai don shi yayi hayar mutane 10 don su yi garkuwa da tsohon har fadar sa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel