Da Duminsa: Mutane da Dama Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga Daga Zamfara Suka Faɗa Sansanin Sojoji

Da Duminsa: Mutane da Dama Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga Daga Zamfara Suka Faɗa Sansanin Sojoji

  • Cikin rashin sani wasu miyagun yan bindiga da suka tsero daga Zamfara da Katsina sun faɗa cikin sansanin sojoji
  • Rahoto ya bayyana cewa an ɗauki dogon lokaci ana fafatawa tsakanin miyagun da sojoji a ƙauyen Maganda
  • Soja ɗaya ya ɓata yayin da yan bindiga da dama suka mutu, wasu suka tsere cikin dazuzzuka da raunin harbi

Niger - Wasu yan bindiga da suka yi kokarin tserewa daga ruwan wutar sojoji a Zamfara da Katsina sun kwashi kashin su a hannun jami'an soji a ƙauyen Maganda, ƙaramar hukumar Shiroro, jihar Neja.

Miyagun, waɗanda suka yi kokarin tserewa ta sanannen dajin Allawa cikin ɗaruruwansu, sun faɗa sansanin sojoji, inda suka fafata na tsawon awanni.

Jaridar Punch ta ruwaito cewa yayin wannan gurmurzu soja guda ɗaya ya bata bayan kammala musayar wuta.

Kara karanta wannan

‘Yan bindiga suna sulalewa zuwa makwabta yayin da Sojoji suka rutsa Zamfara da ruwan wuta

Sojoji sun hallaka yan bindiga da dama a Naja
Da Duminsa: Mutane da Dama Sun Mutu Yayin da Yan Bindiga Daga Zamfara Suka Faɗa Sansanin Sojoji Hoto: punchng.com
Asali: UGC

Wane sakamako yan bindiga suka samu?

Rahoto ya nuna cewa sojoji sun hallaka yan bindigan da dama yayin da wasu suka tsere cikin daji da raunin harbi a tattare da su.

Bugu da ƙari sojojin ba su kyale waɗanda suka gudu da harbin bindiga ba, inda suka mamaye dajin domim binciko su.

Hakanan kuma dakarun sojin sun kwato makamai da suka haɗa da manyan bindigun jigida guda 6, AK-47 da yawa da kuma buhunan alburusai.

Shin hari yan bindigan suka kaiwa Sojoji?

Wani mutumi daga yankin Alawa yace:

"Maganar gaskiya gawarwakin da muka gani na baƙi ne, dukka suna da dogon gashi kamar na mata kuma ba su yi kama da yan Najeriya ba."
"Basu san wurin ba, shiyasa suka faɗa sansanin sojojin. Ga dukkan alamu basu san cewa mazaunin sojoji suka shiga ba."

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun cafke wadanda suka kashe mahaifin tsohon gwamnan Filato

A watan Afrilu, yan bindiga sun kai hari sansanin sojoji dake Alawa, inda suka hallaka jami'ai akalla biyar sannan suka kone wurin baki ɗaya.

A wani labarin kuma yan majalisun PDP sun maka kakakin Majalisa a Kotu, Sun ce an rike musu hakkokinsu don sunki komawa APC

Mambobin jam'iyyar PDP bakwai daga cikin yan majalisar dokokin jihar Cross Ribas, waɗanda basu sauya sheka zuwa APC ba, sun maka kakakin majalisa da wasu mutum 17 a kotu.

Yan majalisun sun shigar da ƙara gaban kotun ne da bukatar a biya su hakkokinsu da aka rike, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel