'Yan sanda sun cafke wadanda suka kashe mahaifin tsohon gwamnan Filato
- 'Yan sanda asun cafke wasu bata-gari da ake zargin su suka hallaka mahaifin tsohon gwamnan jihar Filato
- A baya 'yan bindiga sun sace mahaifin gwamnan, inda suka boye shi kana suka hallaka shi
- A halin yanzu an gabatar da mabarnatan ga manema labarai inda suka tabbatar da yadda suka hallaka marigayin
Plateau - Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta cafke wadanda suka kashe Pa Defwan Dariye, mahaifin tsohon gwamnan jihar Filato, Joshua Dariye, inji rahoton jaridar Punch.
An kashe dattijon dan shekara 93 bayan da masu garkuwa da mutanen suka sace shi suka kuma karbi kudin fansa miliyan 10 daga iyalansa.
Jagoran gungun masu garkuwa da mutane, Jethro Nguyen, dan shekara 53, ya ce ya dauki hayar wasu mutane 10 ciki har da wasu Fulani makiyaya don sace tsohon a gidansa, ya kara da cewa sun tsare shi a maboyarsu na kusan kwanaki 10 kafin su hallaka shi.
Nguyen, wanda aka gabatar da shi a hedkwatar rundunar yan sanda a Abuja, ranar Laraba 8 ga watan Satumba, ya furta cewa ya ba daya daga cikin 'yan tawagarsa umarnin harbe tsohon.
Ya ce sun yi garkuwa da mamacin ne saboda za su iya samun kudi cikin sauki daga gareshi kasancewar dansa ya taba yin gwamna a jihar Filato, kuma sanata a Najeriya.
Shekara daya bayan sace shi, 'yan bindiga sun sace iyalan dan majalisa a Katsina
Wasu gungun 'yan bindiga sun mamaye garin Kurami, garinsu Ibrahim Aminu Kurami, dan majalisa mai wakiltar mazabar Bakori a majalisar dokokin Katsina, inda suka sace matarsa da 'ya'yansa biyu, Daily Trust ta ruwaito.
Hakan na zuwa ne kusan shekara guda bayan da aka sace dan majalisar da kansa kuma aka tsare shi na tsawon kwanaki har sai da aka biya kudin fansa.
'Yan bindigar sun zo ne akan babura da motoci da misalin karfe 8 na daren ranar Asabar, inda suka tare hanyar Funtua zuwa Katsina na mintuna yayin da ake kokarin sace iyalan dan majalisar a gidansa, in ji wata majiya.
'Yan bindiga sun yi awon gaba da yayan Sakataren Gwamnatin jihar Katsina
A wani labarin, 'Yan bindiga masu garkuwa da mutane sun yi awon gaba da Kabir Muhammad Burkai, yaya ga Sakataren gwamnatin Katsina, Alhaji Mustapha Muhammad Inuwa.
Katsina Post ta ruwaito cewa yan bindigan sun saceshi ne ranar Laraba, 1 ga Satumba, 2021 a gonar sa dake wani kauye mai suna Daftau da rana, karamar hukumar DanMusa ta jihar.
Kabir Muhammad Burkai dai mahaifin su daya da Mustapha Inuwa sai dai ba mahaifiyar su daya ba. Sai dai har ya zuwa lokacin rubuta wannan rahoton, ba’a samu labarin ko an sako shi ba kuma ‘yan bindigar ba su tuntubi yan uwansa ba.
Asali: Legit.ng