Yan Majalisun PDP Sun Maka Kakakin Majalisa a Kotu, Sun Ce An Rike Musu Hakkokinsu Don Sunki Komawa APC

Yan Majalisun PDP Sun Maka Kakakin Majalisa a Kotu, Sun Ce An Rike Musu Hakkokinsu Don Sunki Komawa APC

  • Yan majalisun PƊP a jihar Cross Rivers sun garzaya kotu suna neman a bi musu hakkinsu da kakakin majalisa ya karkatar
  • Yan majalisun sun bayyana wa kotu cewa an rike musu kudadensu ne domin sun ƙi sauya sheka zuwa APC tare da gwamna
  • Kakakin majalisar dokokin yace ba zai faɗi komai ba tun da an kai lamarin gaban kotu

Cross Rivers - Mambobin jam'iyyar PDP bakwai daga cikin yan majalisar dokokin jihar Cross Ribas, waɗanda basu sauya sheka zuwa APC ba, sun maka kakakin majalisa da wasu mutum 17 a kotu.

Yan majalisun sun shigar da ƙara gaban kotun ne da bukatar a biya su hakkokinsu da aka rike, kamar yadda the nation ta ruwaito.

Bugu da kari sun zargi cewa an rike musu hakkokinsu na tsawon watanni tun bayan ƙin amincewarsu na sauya sheka zuwa APC tare da sauran takwarorinsu, waɗanda suka mara wa gwamna Ayade baya.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane huɗu da ƙoƙon kan ɗan adam

Yan majalisun PDP sun maka kakakin majalisa a Kotu
Yan Majalisun PDP Sun Maka Kakakin Majalisa a Kotu, Sun Ce An Rike Musu Hakkokinsu Don Sunki Komawa APC Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Yan majalisun PDP sun shigar da ƙarar ne a kotun dake kan hanyar Moore, Calabar babban birnin jihar, ranar Talata.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Rahotanni sun bayyana cewa kotun da ɗage sauraron karar zuwa ranar 14 ga watan Satumba biyo bayan shigar da bukatar hakan daga mambobin APC.

Wane zargi suke wa kakakin majalisar?

Mambobin na PDP sun zargi kakakin majalisar da kuma manyan jami'an gwamnati da kasafta wasu kuɗaɗen da suke hakkokinsu ne a tsakaninsu.

Yan majalisun na zargin cewa manyan mutanen sun yi hakane a wani mataki na hukunta su, domin sun ki amincewa da sauya sheka zuwa APC.

Ɗaya daga cikin yan majalisun, Efa Esua, ya tabbatar da cewa sun shigar da ƙara a gaban kotu, ya kara da cewa waɗanda aka shigar karar ne suka nemi a ɗage zaman.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP: Zamu Haɗa Karfi da Karfe Domin Ceto Najeriya Daga Hannun Jam'iyyar APC a Zaben 2023

Wane mataki kakakin majalisar zai ɗauka?

Duk wani kokarin jin ta bakin kakakin majalisar dokokin jihar ya ci tura, domin kiran wayar da aka masa taki shiga.

Hakazalika, sakataren watsa labaransa, Hope Obeten, yace mai gidansa ba zai ce komai ba kan lamarin kasancewar an kai maganar kotu.

A wani labarin kuma Jam'iyyar PDP ta lallasa APC, ta lashe zaben cike gurbi a jihar Delta

Babbar jam'iyyar adawa People’s Democratic Party, PDP , ta lashe zaɓen cike gurbi na ɗan majalisar dokokin jihar Delta mai wakiltar Isoko ta kudu mazaba ta ɗaya, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Hukumar INEC ta gudanar da zaɓen ne ranar Asabar a baki ɗaya gundumomi 5 na mazaɓar, domin cike gurbin ɗan majalisar yankin, Mr. Kenneth Ogba, wanda ya kwanta dama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262