‘Yan bindiga suna sulalewa zuwa makwabta yayin da Sojoji suka rutsa Zamfara da ruwan wuta

‘Yan bindiga suna sulalewa zuwa makwabta yayin da Sojoji suka rutsa Zamfara da ruwan wuta

  • Dakarun Sojoji sun shiga jejin Zamfara, suna kokarin ganin bayan ‘Yan bindiga
  • ‘Yan bindigan da suka yi rai, suna shigo wa jihohin makwabta domin samun sauki
  • Gwamnatin Sokoto ta dauki mataki domin toshe ‘Yan bindigan da ke shigo mata

Zamfara - A daidai lokacin da dakarun sojojin Najeriya ke cigaba da kai wa ‘yan bindiga hari a Zamfara, miyagun sun fara tsere wa domin su tsira da ransu.

Rahoton jaridar Daily Trust yace ‘yan bindigan suna ta yin hijira zuwa makwabtansu a halin yanzu.

Garin Dange Shuni a jihar Sokoto yayi iyaka da Zamfara, mazaunan garin sun shaida wa VOA cewa suna ganin ‘yan bindiga suna barko wa daga makwantansu.

Ana ganin 'Yan bindiga a Sokoto

Kara karanta wannan

'Yan bindigan da aka fatattaka daga Zamfara sun sace mutum 20 a Sokoto

Wani Bawan Allah ya shaida wa ‘yan jarida cewa wadannan ‘yan bindiga sun fito a gigice, suna fasa shaguna da gidajen mutane domin su saci abincin da za su ci.

Har ila yau, an samu labari wasu daga cikin ‘yan bindigan sun karbe baburan Bayin Allah domin su samu man fetur da za su sa a cikin na su baburan da suke kai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga cikin wadannan masu hijiran ne jaridar tace suka dauke mutane 20 a Bissalam, a garuruwan Illelar Bissalam da Fajaldu a hanyar Sokoto zuwa Gusau.

‘Yan bindiga
Kayan yakin Sojoji a Zamfara Hoto: Babajide Kolade-otitoju
Asali: Facebook

Wasu daga cikin mutanen nan da aka sace sun yi nasarar kubuta daga hannun ‘yan bindigan.

Wani mataki jihar Sokoto ta dauka?

Da yake magana da VOA, kwamishinan tsaro na Sokoto, Kanal Garba Moyi Isa mai ritaya, ya tabbatar da wannan lamari, amma yace gwamnati ta dauki mataki.

Kara karanta wannan

Katsina: ‘Yan bindiga sun sace kanwar Mataimakin Shugaban Majalisa daf da aurenta

“An toshe duka kananan hukumomi 10 na jihar Sokoto da suke kan iyaka da Katsina, Zamfara da Kebbi da kuma kasar Jamhuriyyar Nijar.”

Kwamishinan tsaron wanda tsohon soja ne, ya yabi kokarin da sojoji suke yi a Zamfara, amma yace ya kamata a ce an rutsa sauran jihohin da ‘yan bindigan suke.

Babu batun toshe layukan waya a Kaduna

Ganin yadda aka toshe layukan waya ake cigaba da kai wa miyagu farmaki a Zamfara, an ji rade-radi sun soma yawo cewa za a toshe hanyoyin sadarwa a jihar Kaduna.

Gwamnatin Kaduna ta karyata wannan, tace idan har akwai bukatar rufe hanyoyin sadarwa, za a sanar. Gwamna Nasir El-Rufai yace zuwa yanzu babu wannan shirin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel