Sanatocin Najeriya sun garzaya Landan don gaishe da Tinubu

Sanatocin Najeriya sun garzaya Landan don gaishe da Tinubu

Yayinda ake dumfarar zaben 2023, manyan jiga-jigan siyasa na garzayawa birnin Landan domin gaida tsohon gwamnan jihar Legas, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.

Sanatocin jam'iyyar All Progressives Congress (APC) sun tafi birnin Landan, kasar Ingila domin gaishe da jagoran jam'iyyar Asiwaju Bola Tinubu, wanda ke jinya yanzu haka.

An yiwa tsohon gwamnan Legas din aikin tiyata ne a gwiwarsa.

Daya daga cikin Sanatan ya bayyana hakan a shafinsa na Facebook.

Sanatocin Najeriya sun garzaya Landan don gaishe da Tinubu
Sanatocin Najeriya sun garzaya Landan don gaishe da Tinubu Hoto: Photo credit: Senator Solomon Olamilekan Adeola, FCA
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daga cikin Sanatocin akwai Sanata Olamilekan Solomon mai wakiltar Legas ta yamma; Sanata Tokunbo Abiru mai wakiltan Legas ta gabas da kuma Sanata Opeyemi Bamidele mai wakiltan Ekiti ta tsakiya.

Sauran sune Sanata Adeyemi Oriolowa mai wakiltar Osun da Sanata Sani Musa na jihar Neja.

Kara karanta wannan

Dalibin Jami'a ya yi garkuwa da dan'uwansa dan shekara biyar a jihar Katsina, ya shiga hannu

Asali: Legit.ng

Online view pixel