Dalibin Jami'a ya yi garkuwa da dan'uwansa dan shekara biyar a jihar Katsina, ya shiga hannu

Dalibin Jami'a ya yi garkuwa da dan'uwansa dan shekara biyar a jihar Katsina, ya shiga hannu

  • Matasa biyu sun shiga hannun hukumar kan garkuwa da karamin yaro
  • Hukumar yan sanda ta bayyanasu gaban manema labarai a Katsina
  • Har yanzu matsalar barandanci da garkuwa da mutane sun zama kaya a wuya a yankin arewa maso yamma

Katsina - Wani dalibin aji 3 a jami'a a Katsina da wani abokinsa sun shiga komar yan sanda kan zargin laifin garkuwa da wani dan shekara biya wanda yake dan'uwa gareshi.

A cewar rahoton AIT, Matasan biyu sun bukaci milyan biyar kudin fansa.

Kakakin yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya bayyana sunan matasan biyu matsayin Aliyu Ibrahim da AbdulRahman Abdullahi.

SP Gambo wanda ya bayyanasu gaban manema labarai yace yan asalin karamar hukumar Dutsinma ne na jihar.

An bayyanasu ne tare da wasu masu laifi daban-daban guda biyar.

Kara karanta wannan

Yanzu-yanzu: An toshe hanyoyin sadarwa na zamani a jihar Katsina

Dalibin Jami'a ya yi garkuwa da dan'uwansa dan shekara biyar a jihar Katsina, ya shiga hannu
Dalibin Jami'a ya yi garkuwa da dan'uwansa dan shekara biyar a jihar Katsina, ya shiga hannu
Asali: Getty Images

Kakakin yan sandan ya ce matasan sun aikata wannan laifi ne sakamakon rashin jituwa dake tsakanin mahaifin yaron da aka sace da mahaifiyarsa.

Ya kara da cewa lokacin da aka tuntubin mahaifin yaron don biyan kudin fansa, yace ba zai biya ba.

Hakan ya taimaka wajen bibiyarsu da kuma damkesu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel