Yankin da Ya Dace Ya fitar da Magajin Shugaba Buhari a 2023, Tsohon Gwamnan Borno Ya Magantu
- Tsohon gwamnan Borno, Ali Modu Sheriff, yace bai dace ace dole wanda zai gaji Buhari daga wani yanki zai fito ba
- Sherrif yace magajin Buhari ka iya fitowa daga kowane yanki matukar yana da abubuwan da yan Najeriya ke bukata
- Jigon APC yace zai nemi zama shugaban jam'iyya amma da sharaɗin idan an kai shugabancin yankin arewa maso gabas
Borno - Tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff, yace wajibi yan Najeriya su cire banbancin addini ko yare domin su zaɓi jagoran da ya dace ya mulki Najeriya a 2023, kamar yadda Punch ta ruwaito.
Sheriff ya faɗi haka ne yayin da ya karbi bakuncin wata ƙungiyar magoya bayan jam'iyyar APC a ofishinsa, ranar Alhamis.
Yace kamata yayi yan Najeriya su zaɓa su darje sannan su tace domin samun wanda zai gaji Buhari da ya dace.
Sheriff yace:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Idan yana can ƙarshen Adamawa ne, zamu fita mu nemo shi, idan kuma ɗan jihar Anambra ne, kamata ya yi mu nemo shi. Ya zama wajibi mu bincika sosai kuma mu samo shugaba nagari."
"Amma ya zama wajibi mu amince wa juna, mu zama ƙasa ɗaya kuma mu ɗauki kanmu dai-dai da kowa. Kuma sai mun amince adalin shugaba zai iya fitowa daga kowane yanki."
"Ba ruwan mu da addininsa, ƙabilarsa ko kuma daga wane yanki ya fito, ba zamu taɓa cin nasara ba matukar ba mu aje irin waɗannan tunanin na yanki-yanki ba."
Akwai babban aiki a gaban APC gabanin 2023
Jigon APC ya ƙara da cewa ya zama wajibi jam'iyya ta yi aiki tukuru fiye da baya idan tana son samun goyon bayan yan Najeriya kuma ta cigaba da mulki a 2023.
Ba Inda Zanje, Nima Zan Ɗanɗani Duk Wahalar da Jama'ata Ke Ciki, Matawalle Ya Soke Duk Wani Fita Zamfara
Sheriff yace bayan shugaba Buhari ya gama zangon mulkinsa a 2023, APC na da bukatar aiki sosai domin ta samu kuri'u miliyan 12m, wanda Buhari ya samu a shekarun baya.
Shin dagaske Modu Sheriff zai nemi shugabancin APC?
Da yake martani kan kiran kungiyoyi na ya nemi shugaban APC na ƙasa, yace zai nema amma bisa sharaɗin an bukaci shugaban ya fito daga yankin arewa maso gabas.
A wani labarin kuma kun ji cewa Daruruwan mambobin jam'iyyar PDP sun sauya sheka Zuwa APC
Ɗaruruwan mambobin jami'iyyar hamayya PDP sun sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki APC a hukumance ranar Laraba a jihar Osun, kamar yadda leadership ta ruwaito.
Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola, shine ya karbi sabbin waɗanda suka sauya shekar tare da mai ɗakinsa da sauran shugabannin APC a jihar.
Asali: Legit.ng