Daruruwan Mambobin Jam'iyyar PDP Sun Sauya Sheka Zuwa APC, Gwamna Ya Tarbe Su

Daruruwan Mambobin Jam'iyyar PDP Sun Sauya Sheka Zuwa APC, Gwamna Ya Tarbe Su

  • Daruruwan yan babbar jam'iyyar adawa PDP sun sauya sheka zuwa APC a hukumance a jihar Osun
  • Daga cikin waɗanda suka sauya shekar akwai tsohon gwamnan jihar da sauran kusoshin PDP a Osun
  • Gwamna Oyetola na jihar Osun tare da shugabannin APC na jiha ne suka karbi sabbin mutanen

Osun - Ɗaruruwan mambobin jami'iyyar hamayya PDP sun sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki APC a hukumance ranar Laraba a jihar Osun, kamar yadda leadership ta ruwaito.

Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola, shine ya karbi sabbin waɗanda suka sauya shekar tare da mai ɗakinsa da sauran shugabannin APC a jihar.

Manyan sanannun mutane daga cikin waɗanda suka suya shekan sun haɗa da, tsohon kakakin majalisar wakilan tarayya, Benedict Alabi, tsohon mataimakin gwamna, sanata Iyiola Omisore.

Kara karanta wannan

Gwamnonin PDP: Zamu Haɗa Karfi da Karfe Domin Ceto Najeriya Daga Hannun Jam'iyyar APC a Zaben 2023

Gwamnan jihar Osun, Adegboyega Oyetola
Daruruwan Mambobin Jam'iyyar PDP Sun Sauya Sheka Zuwa APC, Gwamna Ya Tarbe Su Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Sauran sun haɗa da mai magana da yawun majalisar dattijai, sanata Ajibola Bashiru, da kuma shugaban jam'iyya, Gboyega Famodun.

Manyan yan siyasan sun sauya sheka zuwa APC ne ƙarkashin jagorancin tsohuwar mai bada shawara ta musamman kan tsare-tsare ga tsohon gwamna Olagunsoye Oyinlola, Funmilayo Olasheinde Mustapha.

Ko meyasa suka sauya sheka?

Mustapha, wadda tsohuwar yar majalisar dokoki ce karakashin PDP, ta jagoranci ɗaruruwan magoya bayanta daga mazaɓar Ila, ta bayyana cewa ta fice daga PDP ne saboda rikice-rikicen da ya addabe ta.

Ta kara da cewa duk jam'iyyar da ba zata iya magance damuwar cikin gida ba, to ba zata iya magance ta al'ummar jiha da ƙasa ba.

Bugu da ƙari tace nasarorin da gwamna Oyetola ya samu a cikin shekara uku kacal duk da yanayin matsalar kuɗaɗen da ake ciki sun isa su jawo hankalin mutane.

Kara karanta wannan

Ba Inda Zanje, Nima Zan Ɗanɗani Duk Wahalar da Jama'ata Ke Ciki, Matawalle Ya Soke Duk Wani Fita Zamfara

A wani labarin kuma Gwamnonin PDP sun sha Alwashin haɗa karfi da karfe domin kwace mulki daga hannun APC a 2023

Gwamnonin da suka ɗare kan madafun iko karkashin PDP sun bayyana shirin da suke na kwace mulki daga hannun APC.

Shugaban ƙungiyar gwamnonin, Aminu Tambuwal, yace yanzun kansu a haɗe yake kuma zasu ceto Najeriya daga APC.

Asali: Legit.ng

Online view pixel