Macizai sun addabi jami'ar Katsina, ma'aikata sun shiga atisayen korar macizai

Macizai sun addabi jami'ar Katsina, ma'aikata sun shiga atisayen korar macizai

  • Macizai sun addabi jami'ar Umaru 'Yar Adua dake jihar Kastina, lamarin da yake haifan dardar
  • A halin yanzu, jami'ar ta dauki matakin ci gaba da feshin maganin dabbobi domin fatattakar macizai
  • Jami'an ta bayyana cewa, tana kuma sare bishiyoyi da shukoki domin tabbatar da aminci a jami'ar

Katsina - Hukumar jami’ar Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina, a ranar Talata 7 ga watan Satumba, ta ce ta yi feshin magani a babbar harabar jami’ar don kubuta daga macizai da sauran nau'ikan dabbobi wadanda ka iya cutar da dalibai da sauran membobin jami'ar.

A karshen makon da ya gabata, wani faifan bidiyo da ke nuna wani kumurcin maciji da aka kama a cikin Sabbatical Quarters na jami'ar ya yadu a kafafen sada zumunta, Punch ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Jami'ar Nigeria ta fatattaki Lakcara mai koyar da turanci saboda baɗala

Macizai sun addabi jami'ar Katsina, ma'aikata sun shiga atisayen korar macizai
Jami'ar Umaru Musa 'Yar Adua dake Katsina | Hoto: free-apply.com
Asali: UGC

A cikin wata sanarwa a ranar Talata mai dauke da sa hannun Shugaban Hulda da Jama’a na jami'ar, Mallam Abdulhamid Danjuma, ta ce an yi feshin magani a harabar jami'ar.

Sanarwar ta karanta a wani bangare:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

“A kokarin kawar da macizai da sauran dabbobi masu rarrafe a cikin harabar gaba daya, gudanarwar jami’ar Umaru Musa Yar’adua ta Jihar Katsina, ta yi nasarar korar dimbin macizai a cikin harabar cibiyar.
"Kokarin ya yiwu ne ta hanyar daya daga cikin atisayen da ake yi na yau da kullum da ake gudanarwa a cibiyar.
“A ka’ida, hukumomin jami’ar galibi suna gudanar da atisayen feshin magani bayan mako biyu don fatattakar dabbobi masu rarrafe, macizai da sauran kwari don sanya jami’ar zama wuri mai aminci ga ma’aikata, dalibai da baki.
“Baya ga feshin maganin, ana sassare bishiyoyi da shukoki don kawata kewayen jami’ar da korar dabbobi masu rarrafe da sauran beraye saboda membobin jami’ar su sami kwanciyar hankali da tafiya cikin walwala ba tare da wani fargaba ba.

Kara karanta wannan

Zamfara: Iyayen daliban da aka sace sun shiga mawuyacin hali bayan katse layukan waya

Hakazalika, sanarwar ta bukaci dalibai da sauran mazauna jami'ar da su kasance masu kai rahoto ga hukumar makaranta duk lokacin da suka ga wani abu da basu fahimta ba na dabbobi kasancewar ana tsakiyar damina.

A bangare guda, jami'ar ta ba da tabbacin kare rayuka da lafiyar mazauna jami'ar, inda sanarwar ta ce:

“Jami’ar tana ba da tabbacin cewa za ta ci gaba da kare rayukan ma’aikatanta, dalibai da sauran baki ta hanyar yin aiki tukuru don magance duk kalubalen da ke iya zama barazana ga rayuwar cikin harabar.”

Mutumin da sana'arsa kenan yawo da dubban kudajen zuma a jikinsa

Yayin da ake korar dabbobi a Ktsina, a wata kasa kuwa an samu mutumin da sana'arsa kenan yake yawo da kudajen zuma jikinsa, kuma ba tare da sun cije shi ba.

An ce harbin kudan zuma na iya haifar da kumburin jiki da tsananin zogi har ya kai ga rashin lafiyan da zai bukaci kulawar likita. Wannan yasa mutane da dama ke gudun kusantar wadannan kwari masu hadari.

Kara karanta wannan

Barazanar tsaro: Jihar Adamawa ta rufe makarantu 30 na kwana saboda rashin tsaro

Amma sabanin haka, an samu wani mutum da ya mayar da jikinsa wurin ajiyar kudajen zuma kuma sana'a mai romon riba, lamarin da ya kasance sabo ga jama'a.

Mutumin ya shahara a garinsu saboda iya yawo da yake da dubban kudajen zuma a jikinsa ba tare da wani kariya na jiki ba.

Wani bidiyon YouTube na Afrimax ya nuna yadda mutumin ya aikata abin ban mamaki na yawo da kudan zuma.

Miyetti Allah za ta tura Fulani makiyaya Amurka domin a horar dasu kiwon zamani

A wani labarin na daban, Amina Ajayi, Jakadiyar Kungiyar Miyetti Allah Kautal Hure, kungiyar raya al'adu, ta gabatar da wani shiri mai karfi na horar da Fulani makiyaya akan kiwo na zamani, wanda aka misalta shi da kwatankwacin kiwo a Amurka.

Ajayi ta bayyana hakan ne a cikin jawabinta na karbar mukami biyo bayan nada ta a matsayin Jakadiyar Miyetti Allah a hedikwatar kungiyar ta kasa da ke Uke, Karamar Hukumar Karu ta Jihar Nasarawa.

Kara karanta wannan

Tsaro: Gwamnati ta ba da umarnin a katse sabis din layukan waya a Zamfara

Ta bayyana cewa rukunin farko na masu horaswa da malamai na makarantar Miyetti Allah Cattle Ranch Academy zai yi tafiya zuwa California a kasar Amurka, a farkon 2022, Vanguard ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.