Jami'ar Nigeria ta fatattaki Lakcara mai koyar da turanci saboda baɗala

Jami'ar Nigeria ta fatattaki Lakcara mai koyar da turanci saboda baɗala

  • Jami'ar Obafemi Awolowo University, da ke Ile-Ife ta sallami wani lakcara mai suna Dr Adebayo Mosobalaje
  • An kore Dr Mosobalaje ne bayan samunsa da laifin badala da wata daliba a makarantar
  • Majalisar kolin Jami'ar ta ce an kafa kwamitin bincike kuma sun tabbatar da laifin don haka aka kore shi kamar yadda dokar jami'ar ta tanada

Ibadan, Oyo - An sallami Dr Adebayo Mosobalaje, malami a tsangayar koyar da harshen turanci a Jami'ar Obafemi Awolowo University, da ke Ile-Ife saboda badala, Daily Trust ta ruwaito.

Vanguard ta ruwaito cewa Mahukunta a makarantar sun amince da korarsa daga aiki ne bayan an same shi da laifin cin zarfin wata daliba a jami'ar.

Jami'ar Nigeria ta fatattaki Lakcara mai koyar da turanci saboda baɗala
Jami'ar Obafemi Owolow. Hoto: Daily Nigerian
Asali: Facebook

Mai magana da yawun jami'ar, Abiodun Olarewaju ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

Kara karanta wannan

Shugaban kasa ya yi sabon nadi, ya ba Osinbajo sabon aiki, ya nada shugaba a hukumar NCDC

Sanarwar ta ce:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"A yunkurinta na kawar da dukkan wani nau'i na badala, cin zarafi da tursasawa a jami'ar, mahukunta a Jami'ar Obafemi Awolowo University, Ile-Ife, ta sake korar wani lakcara da aka samu da laifin cin zarafin daliba.
"An cimma matsayar korar Dr Adebayo Mosobalaje na tsangayar koyar da harshen turanci ne yayin taron majalisar kolin jami'ar na karshe da aka yi a ranar Talata 7 ga watan Satumban 2021.
"Bayan tattaunawa sosai kan rahoton kwamitin koli na jami'ar, wacce ta yi bincike kan zargin badalar da ake yi wa Mosobalaje, Jami'ar ta bayyana cewa ba za ta amince da duk wani nau'in badala ba hakan yasa jami'ar ta dauki matakin kamar yadda ya ke a dokarta."

Jigawa: Hotunan Auren Yaya Da Ƙanwa da Kotun Shari’ar Musulunci Ta Aurar da Su Duk da Ƙin Amincewar Mahaifinsu

Kara karanta wannan

Jami'ar Nigeria ta dakatar da farfesan da ake zargi da ƙaryar rage shekarunsa

A wani labarin daban, wata babban kotun Shari'a a ƙaramar hukumar Hadejia na Jihar Jigawa, a ranar Alhamis, ta aurar da wasu mata biyu ƴaƴa da ƙanwa, Premium Times ta ruwaito.

An aurar da matar biyu ne bayan mahaifinsu, Abdullahi Malammmadori, ya ƙi aurar da su duk da wa'adin kwanaki 30 da kotun ta bashi amma bai aurar da su ba.

Shugaban wata gidauniya na taimakon mata, marayu da marasa galihu, Fatima Kailanini, ta yi ƙarar Mr Malammadori kan ƙin aurar da Khadijat da Hafsat Abdullahi duk da sun fito da waɗanda suke so.

Asali: Legit.ng

Online view pixel