Zaɓen ƙananan hukumomi: Nasarar da PDP ta yi a akwati na ya nuna APC bata yi maguɗi ba, El-Rufai

Zaɓen ƙananan hukumomi: Nasarar da PDP ta yi a akwati na ya nuna APC bata yi maguɗi ba, El-Rufai

  • Gwamnan jihar Kaduna Nasir El-Rufai ya ce kayan da APC ta sha a akwatinsa ya nuna jam'iyyar bata yi magudi ba
  • Gwamna El-Rufai ya kuma ce masu zargin cewa gwamnati ta tsara wani yaudara da na'urar zaben sun ji kunya
  • El-Rufai ya ce sakamakon zaben ya kuma nuna cewa kan mutanen Kaduna ya hadu sun fara zaben cancanta da aiki ba wai jam'iyya ba

Kaduna - Nasir El-Rufai, gwamnan jihar Kaduna ya ce nasarar da jam'iyyar PDP ta samu na lashe zabe a akwatinsa ya nuna cewa APC bata yi maguɗi ba da na'urar zabe na zamani, rahoton The Cable.

A ranar 4 ga watan Satumba, hukumar zabe na jihar Kaduna, KADSIECOM, ta yi zabe ta hanyar amfani da na'urar mai amfani da lankarki.

Kara karanta wannan

An kuma: PDP ta sake lallasa APC a jihar Kaduna a zaben kananan hukumomi a Jaba

Zaɓen ƙananan hukumomi: Nasarar da PDP ta yi a akwati na ya nuna APC bata yi maguɗi ba, El-Rufai
Gwamnan Jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Kafin wannan lokacin, Jihar Kaduna ce ta farko da ta fara amfani da wannan sabon tsarin zaben na zamani a Nigeria.

Sai dai, jam'iyyar APC ta sha kaye a akwatin El-Rufai yayin zabukan kananan hukumomi da aka gudanar a ranar Asabar a jihar.

Idan da mun yi magudi ba zan fadi a akwati na ba, El-Rufai

Da ya ke magana a shirin Sunrise Daily na gidan talabijin din Channels a ranar Litinin, El-Rufai ya ce sakamakon zaben ya nuna cewa jam'iyyar mai mulki ba ta yi magudi ba wurin tsara na'urar zabukan kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Ya kuma ce sakamakon ya nuna babu rabuwan kai a jihar sannan, ya kara da cewa hakan hujja ne da ke nuna mutane sun fara yin zabe bisa aikin da wadanda suka zaba suka yi.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: An Kashe Mutane 3 a Sabon Harin Da Aka Kai a Plateau

Ya ce:

"Wadanda suka kai rahoto cewa an sauya tsarin na'urar don yin magudi zun ji kunya a lokacin da aka ruwaito cewa APC ta sha kaye a akwati na. Mutane na dariya cewa na sha kaye a akwati na amma demokradiyya ce ta yi aiki."
"Ba suna na bane a takardan zaben don haka ba hujja bane a kai na, hukka ne kan kansilar da shugaban karamar hukuma. Rashin nasara a akwatin zabe na ya nuna cewa ba mu yi magudi ba ko lalata na'urar, ba mu yi wa hukumar zabe mai zaman kanta na jihar mu katsalandan ba kuma komai ya tafi dai-dai.
"Sakamakon zaben kawo yanzu ya nuna kan mutanen mu ya hadu dama shine abin da muke aiki a kai. Muna son mu canja yadda wasu ke dauka cewa jam'iyyar PDP na wani bangare ne a jihar, wani sashin kuma na APC. Wasu na cewa PDP na da alaka da wani addini, APC ma na da alaka da wani addini.

Kara karanta wannan

Rikicin Jos: El-Rufa'i ya yi alkawarin magance matsalar tsaro a Jos da Kaduna

"Sakamakon zaben ya nuna cewa daga karshe dai mun hada kan mutanen Kaduna kuma mutane suna zabe bisa cancanta da aikin da wadanda suka zaba suka yi."

Tsaro: Gwamnatin Kaduna ta hana yawon gararamba da ayyukan sare itatuwa a dazukan jihar

A wani labarin daban, Gwamnatin Jihar Kana ta haramta yawon 'gararamba' a gari da shiga manyan dazuka a jihar domin yin ayyuka, The Cable ta ruwaito.

Jihar ta kuma hana sare itatuwa domin yin aikin kafinta, girki da gawayi a kananan hukumomi bakwai a jihar saboda karuwar matsalar rashin tsaro.

Kwamishinan harkokin cikin gida da tsaro na jihar Samuel Aruwan ne ya bada sanarwar a ranar Talata kamar yadda The Cable ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Online view pixel