Jihar Bauchi: Gwamna Bala Mohammed ya rantsar da sabbin kwamishinoni

Jihar Bauchi: Gwamna Bala Mohammed ya rantsar da sabbin kwamishinoni

  • Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya rantsar da sabbin kwamishinoni 21
  • Hakazalika gwamnan ya rantsar da sabon Sakataren Gwamnatin Jihar, Shugaban Ma’aikata da Babban Sakatare mai zaman kansa
  • Babbar alkalin jihar, Jastis Talatu Umar ce ta rantsar da su a yau Alhamis, 2 ga watan Satumba

Bauchi - Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya nada sabbin kwamishinoni 21.

Babbar alkalin jihar, Jastis Talatu Umar ce ta rantsar da sabbin kwamishinonin a ranar Alhamis, 2 ga watan Satumba a Bauchi, jaridar The Nation ta ruwaito.

Jihar Bauchi: Gwamna Bala Mohammed ya rantsar da sabbin kwamishinoni
Gwamna Bala Mohammed ya rantsar da sabbin kwamishinoni 21 Hoto: sunnewsonline.com
Asali: UGC

Gwamnan ya umarci kwamishinonin da su tabbatar da sanya al'umman kananan hukumominsu cikin ayyukansu da nufin tabbatar da ci gaba da dorewar mulkin.

Ya ce gwamnatinsa za ta ci gaba da ba da fifiko ga kwamishinonin a matsayin masu ruwa da tsaki a siyasar jihar, yana mai cewa:

Kara karanta wannan

Gwamnatin Buhari ta yi nasarar kwato N1trn na kudin sata, Shugabannin APC

"Nadin naku ya dogara ne kan nasarar da kuka samu a siyasa da kuma mutuncin ku"

Ya umarci kwamishinonin da su girmama dukkan hukumomin da aka kafa, musamman Majalisar Dokokin jihar, duba da rawarsu a kundin tsarin mulki da kuma abin da ya kunsa, yana mai cewa mafi yawan mambobin sun fito ne daga jam’iyyar adawa ta APC.

Mohammed ya yi bayanin cewa duk da cewa kusan mafi yawan membobin majalisar sun fito ne daga APC, alaƙar da ke tsakanin bangaren zartarwa da majalisar ta kasance mai daɗi.

Ya ce gwamnatinsa a cikin watanni 33 da suka gabata ta aiwatar da ayyukan raya kasa yayin da ta yaba wa sarakunan gargajiya saboda goyon bayan da suke baiwa gwamnatin a kai a kai musamman a lokacin da ake fama da annobar COVID-19.

Kara karanta wannan

Lalong ya rufe majalisar jihar Filato don hana tsige shi? Gwamnan ya bayyana gaskiyar lamari

Jaridar Punch ta kuma ruwaito cewa gwamnan ya kuma rantsar da Ibrahim Kashim a matsayin Sakataren Gwamnatin Jihar, Aminu Gamawa a matsayin Shugaban Ma’aikata, da Samaila Burga a matsayin Babban Sakatare mai zaman kansa.

Gwamna Mohammed ya rusa tsohuwar majalisarsa a watan Yuni don shigar da 'yan siyasa cikin bangaren zartarwa na gwamnati.

A wani labari na daban, wata babbar kotu da ke zaune a Asaba, babban birnin jihar Delta, ta dakatar da taron karamar hukuma na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) da aka shirya yi ranar 4 ga Oktoba, 2021.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kotun ta kuma hana Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe daga daukar kansa a matsayin shugaban riko na jam'iyyar All Progressives Congress (APC) har sai an yanke hukunci.

A cewar The Guardian, mataimakin shugaban jam’iyyar APC, Olorogun Elvis Ayomanor, wanda ya jagoranci wasu jami’an jam’iyyar APC na Delta, ya garzaya kotu biyo bayan babban taron mazabu na ranar 10 ga watan Yuli, 2021, wanda ake zargin an janye.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kaduna ta haramta cin kasuwannin mako-mako a kananan hukumomi biyar

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng