Rashin tsaro: IGP Baba ya bayyana yadda ya zama shugaban yan sanda a mawuyacin lokaci
- Babban sufeton 'yan sanda na kasa (IGP), Usman Alkali Baba, ya sake jaddada aniyarsa na kawo karshen rashin tsaro a kasar
- IGP Usman Alkali Baba ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ne ya nada shi a mawuyacin lokaci
- A cewarsa, nan ba da jimawa ba za a dauki sabbin 'yan sanda 20,000 don inganta karfin rundunar
FCT, Abuja - Sufeto Janar na 'yan sanda (IGP), Usman Alkali Baba, ya ce ya karbi ragamar jagorancin rundunar a wani mawuyacin lokaci.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya nada Baba a lokacin da aka yi tawaye na haramtacciyar Kungiyar ‘Yan asalin yankin Biyafara (IPOB) a watan Afrilu.
Legit.ng ta tattaro cewa tsagerun sun yi kaca -kaca a lokacin inda suka kona ofisoshin 'yan sanda tare da sakin fursunoni.
Da yake magana lokacin da ya ziyarci Gwamna Bello Masari na Katsina, Baba ya bayyana wasu kalubalen da rundunar ke fuskanta.
A cewarsa, nan ba da jimawa ba za a dauki sabbin 'yan sanda 20,000 don inganta karfin rundunar.
Yace:
“Na shigo a matsayin IGP a mawuyacin lokaci. Lokacin da na zo, a Kudu maso Gabas da Kudu maso Kudu ne aka yi ta kashe-kashe da suka hada da kashe jami'an tsaro da kuma lalata wuraren aikinmu.
"Yayin da kudu maso kudu da kudu maso gabas ke samun kwanciyar hankali, halin da ake ciki a arewa maso tsakiya da arewa maso yamma na kara yin muni. Za mu dauki ma'aikata daga kowace karamar hukuma a kasar nan. Umurnin shugaban kasa ne cewa ya kamata mu dauki 10,000 don 2020 da kuma wasu 10,000 don 2021."
Tun farko a cikin sakonsa, Masari ya ce gwamnatinsa tana kokarin daukar karin ‘yan banga domin karfafa tsaro a jihar.
Gwamnan ya ce 'yan sanda ba su da isassun ma'aikata da kayan aiki don tabbatar da tsaro a jihar, ya kara da cewa za a dauki yan banga a dukkan kananan hukumomi 34 na jihar.
Masari ya ce:
"Daga kiyasin da na yi wa 'yan sanda a kananan hukumomin, ba na tsammanin muna da' yan sanda 3,000 a cikin jihar baki daya."
A wani labari, mai Martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya koka kan karuwar harin yan bindiga, yana mai cewa kisar gillar da aka yi wa mace mai juna biyu a Zaria a matsayin abin damuwa.
Daily Trust ta ruwaito cewa sarkin ya ce kasar na cikin wani lokaci mai wahala, yana mai cewa matsalar ba Nigeria kadai ta shafa ba.
Asali: Legit.ng