Rufe Makarantun Kaduna: Iyayen Ɗalibai Sun Ce Sun Fara Tura Ƴaƴansu Koyon Ɗinki Da Walda

Rufe Makarantun Kaduna: Iyayen Ɗalibai Sun Ce Sun Fara Tura Ƴaƴansu Koyon Ɗinki Da Walda

  • Iyayen yara a Kaduna sun bayyana cewa suna tura yaransu zuwa koyon sana'o'i a yayin da makarantun jihar ke rufe
  • Wani iyayen sun bayyana cewa yaransu na koyon sana'o'i kamar dinki da walda da wasu sana'o'in da za su amfane su
  • Wasu iyayen yaran sun kuma ce suna koyar da yaransu karatu a gida tare da shawartar gwamnati ta rika koyar da yaran ta talabijin

A yayin da Gwamna Nasir El-Rufai na Jihar Kaduna ya rufe makarantun jihar sakamakon sace-sacen dalibai da masu garkuwa ke yi, iyayen yara sun fara tura su wuraren koyon sana'o'i, rahoton Peoples Gazette.

A ranar 6 ga watan Agusta ne Gwamnatin Mallam Nasir El-Rufai ta sanar da dage komawa makarantun har wani lokaci a nan gaba.

Kara karanta wannan

Gwamnan Neja ya gana da daliban Tegina 91 bayan kwanaki 88 da sukayi hannun yan bindiga

Rufe Makarantun Kaduna: Iyayen Ɗalibai Sun Ce Suna Tura Ƴaƴansu Koyon Ɗinki Da Walda
Gwamnan Kaduna Nasiru El-Rufai. Hoto: Peoples Gazette
Asali: Facebook

Gwamnati ta ce rufe makarantun ya fi zama alheri ga yaran makarantan a yayin da sace dalibai don karbar kudin fansa ke kara yawaita musamman a yankin arewa.

Ibrahim Yusuf, wani mutum mai 'ya'ya biyu, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na NAN a ranar Juma'a a Kaduna cewa tsare yaran ya fi muhimmanci don haka ya bukaci gwamnati ta rika amfani da rediyo, talabijin da soshiyal midiya don koyar da yara a gida.

Mr Yusuf ya bayyana cewa bai bar yaransa kara zube ba a gida. A cewarsa, suna zuwa shagonsa tare da shi suna koyon walda kamar yadda Peoples Gazette ta ruwaito.

Wata mahaifiya, Hauwa Muhammad, ta ce ta tura danta mai shekara 10 zuwa wurin koyon dinki.

Ta yabawa gwamnatin jihar Kaduna bisa daukan matakin kare yaran tana mai kira ga gwamnatin ta inganta tsaro domin daliban su samu damar komawa makaranta.

Kara karanta wannan

Daliban Islamiyya ta Tegina 5 na cikin mawuyacin hali – Shugaban makarantar

Ina koyar da yara na karatu a gida, wani mahaifin dalibai

Kazalika, Abel ya bayyana cewa yana koyar da yaransa idan ya dawo daga aiki karfe 4 na yamma sannan yana basu karatun da za su yi idan baya nan don kada su yi zaman banza.

Ya bukaci iyaye kada su kyalle yaransu su rika yawon gararamba a gari amma su basu kariya sannan su rika koyarda su tare da koya musu ayyukan gidan.

Har cikin silin na ke ɓoye kuɗi amma tana shiga ta sace: Miji ya nemi a raba aure don satar da matarsa ke masa

A wani labarin daban, wata kotun gargajiya mai zamanta a Igando a jihar Legas, a ranar Alhamis ta tsinke auren mata da miji da suka shafe shekaru 10 suna zaman aure saboda halin sata da matar ke da shi, Premium Times ta ruwaito.

Mutiu Bamgbose, dan kasuwa mai shekaru 45, ya kuma zargi matarsa Aliyah da cin amanarsa na aure.

Kara karanta wannan

Da Ɗumi-Ɗumi: Sabon harin Jihar Benue ya yi ajalin rayukan mutane 8

Da ya ke yanke hukunci, alkalin kotun, Adeniy Koledoye, ya ce babu tantama auren na su ba mai gyaruwa bane duba da cewa wacce aka yi karar ta ta ki amsa gayyatar kotun, Daily Nigerian ta ruwaito.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164