‘Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai da dama a wata makaranta a jihar Zamfara

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai da dama a wata makaranta a jihar Zamfara

  • 'Yan bindiga sun kai hari wata makaranta da ke karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara
  • An tattaro cewa maharan sun yi awon gaba da daliban makarantar da dama
  • Mummunan al'amarin ya afku ne a safiyar yau Laraba, 1 ga watan Satumba

Labari da muke samu a yanzu daga jihar Zamfara ya nuna cewa wasu ‘yan bindiga da ake zaton masu garkuwa da mutane ne sun kai farmaki wata makaranta da ke karamar hukumar Maradun.

An tattaro cewa maharan sun kuma yi awon gaba da wasu dalibai da dama a makarantar wacce take ta maza da mata a hade.

‘Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai da dama a wata makaranta a jihar Zamfara
‘Yan bindiga sun yi garkuwa da dalibai da dama a wata makaranta a jihar Zamfara Hoto: Governor Bello Matawalle
Asali: Facebook

Sashin Hausa na BBC ta ruwaito cewa mazauna garin Kayan Maradun sun sanar da ita cewa lamarin ya afku ne a safiyar ranar Laraba, 1 ga watan Satumba. Sun kuma bayyana cewa ba a san adadin daliban da maharan suka sace ba.

Kara karanta wannan

Kawar dan sanatan da aka kashe ta bayyana abubuwan da suka faru kafin muyuwarsa

Kafar labaran ta kuma ruwaito cewa sama da dalibai 400 ne a makarantar a yayin da aka kai farmakin, inda aka ce daliban na rubuta jarrabawar Mock ne lokacin da lamarin ya afku.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wani malamin makarantar ya ce:

"Muna shirye-shiryen yin jarrabawar mock ta 'yan aji biyar, bayan mun fito mun yi wa 'yan SS II bayani mun fito mun tunkaro dakin malamai, muna zaunawa sai kawai muka ji kukan babura sun tunkaro makaranta."

Ya ce daga nan ne suka watse suka shiga cikin gonar gero tare da wasu daliban amma duk da haka 'yan bindigar sun kwashe dalibai da dama.

Gwamnatin Zamfara ta ba da umarnin rufe kasuwanni da tashoshin man fetur

A baya mun kawo cewa an rufe dukkan manyan kasuwannin jihar Zamfara sakamakon umarnin Gwamna Bello Matawalle.

Kara karanta wannan

Tirkashi: Gwamnan APC na fuskantar barazanar tsigewa kan rikicin makiyaya

Kamar yadda gidan talabijin na Channels TV ya ruwaito, gwamnan ya kuma bayar da umurnin rufe dukkan gidajen mai dake yankunan. Ya kuma ba da umarnin cewa kada a sayar da mai ko da a cikin jarkoki.

TVC News ta rahoto cewa Matawalle ya ce matakin ya zama dole idan aka yi la’akari da dawowar fashi da makami da garkuwa da mutane a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng