Idan babu namijin da ya furta maki so, ki yi amfani da asiri, wata budurwa ta bayar da shawara a bidiyo

Idan babu namijin da ya furta maki so, ki yi amfani da asiri, wata budurwa ta bayar da shawara a bidiyo

  • Wani gajeren bidiyo na wata 'yar Najeriya da ta nemi mutane su yi amfani da asiri wajen samun soyayyar namiji ya sa mutane tofa albarkacin bakunansu
  • Ifeoma ta bayyana cewa hanya daya tilo da ‘yan matan da suka rasa samun kulawa ta soyayya za su bi shi ne hadawa da asiri
  • Mutumin da ke kusa da ita, yayin da ta ke ba da shawarar, ya yi mamakin dalilin da ya sa samun masoyi ya zama abu mai mahimmanci

Wata budurwa a dandalin sada zumunta na Instagram, Nwachukwu Ifeoma Esther, ta tayar da kura sosai a kafafen sada zumunta bayan ta yi wani jawabi mai rikitarwa a yanar gizo.

A wani wallafa da tayi a Instagram, matar ta shawarci ‘yan mata da su yi amfani da asirin idan babu wani namiji da ya furta cewa yana son su.

Kara karanta wannan

Rikicin Jos: Wasu Migayu Ne Ke Amfani Da Addini Da Siyasa Don Ganin Ba a Zauna Lafiya Ba a Plateau, Lalong

Idan babu namijin da ya furta maki so, ki yi amfani da asiri, wata budurwa ta bayar da shawara a bidiyo
Budurwa ta shawaci 'yan mata da su yi amfani da asiri idan suka rasa masoyi Hoto: @esthersky_77
Asali: Instagram

Yayin da take zaune kusa da masoyinta, budurwar ta nanata abin da ta faɗa, tana mai cewa amfani da asiri shine babban mafita a irin wannan yanayin.

Da yake martani, mutumin da ke kusa da ita ya yi ihu yana tambayar me zai sa mutum ya yi haka. Cikin barkwanci, ta nemi saurayinta ya so asiri.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kalli bidiyon a kasa:

Lokacin da shafin @Instablog9ja ya sake yada bidiyon akan dandamalin, ya haifar da dubban martani. Legit.ng ta tattara wasu daga ciki a kasa:

Laffdoctor ya ce:

"Wannan shekarar ba ta ƙare ba amma nayi amfani da takardu 6 cike ... Nasiha ta ko'ina."

zahara_yusuf ta ce:

“Idan kin yi amfani da asiri a kan wani mutum, toh wannan gurbi ba naki bane.”

nita_oamen ya yi mamaki:

Kara karanta wannan

Kawar dan sanatan da aka kashe ta bayyana abubuwan da suka faru kafin muyuwarsa

"Kun ji wani shirmen da ke fitowa daga bakin mace?"

A wani labari, hamshakin attajirin nan na Najeriya, Marksman Chinedu Ijiomah ya da’da’da zukatan mutane da dama a shafukan sada zumunta yayin da ya yiwa wasu mutane alkhairi.

Marksman ya rarraba kayan tallafi na tsabar kuɗi da kayan abinci ga sama da mutane 120.

A wani rubutu da ya yi a shafin Facebook a ranar Litinin, 23 ga watan Agusta, shugaban Kamfanin Chinmark Group ya bayyana cewa bayar da taimako ga mutane shine mabuɗin inganta rayuwar al'umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng