Hukumar yan sanda ta bayyana adadin daliban da aka sace a jihar Zamfara yau
- Kuma dai, yan sanda sun tabbatar da awon gaba da gomman dalibai a Zamfara
- Wannan ya biyo bayan sako daliban makarantar noma a makon da ya gabata
- Gwamnan jihar ya bada umurnin rufe dukkan makarantun jihar gaba daya
Zamfara - Hukumar yan sandan jihar Zamfara ta bayyana adadin daliban da aka sace a makarantar GDSS Kaya dake karamar hukumar Maradun ta jihar a ranar Laraba.
Kakakin hukumar yan sandan jihar, Muhammadu Shehu, a jawabin da ya saki yace yara 73 yan bindigan suka dauke, TVC ta ruwaito.
Yace:
"Hukuma na tabbatar da sace dalibai 73 na makarantar GDSS Kaya dake karamar hukumar Maradun."
"Wannan ya biyo bayan harin da wasu gungun yan bindiga suka kai makarantar misalin karfe 11:22am."
A riwayar Premium Times, Shehu ya kara da cewa kwamishanan yan sandan jihar ya tura jami'ansa domin ceto wadannan dalibai.
A cewarsa:
"Hukumar karkashin jagorancin CP Ayuba N Elkanah ta tura rundunar cetosu kuma suna tare da jami'an Sojoji domin tabbatar da cewa an ceto yanar."
Gwamnatin Zamfara ta sanya dokar ta baci, ta kulle dukkan makarantun jihar
Gwamnatin jihar Zamfara ta sanya dokar ta baci a fadin kananan hukumomi 14 dake jihar.
Hakazalika gwamnatin ta kulle dukkan makarantun gwamnati da masu zaman kansu dake dukkan kananan hukumomin jihar.
Wannan ya biyo bayan harin da yan bindiga suka kai garin Kaya, karamar hukumar Maradun ta jihar da dafiyar Laraba inda suka yi awon gaba da daliban makaranta.
A cewar TVCNews, dokar ta bacin zata kama ne daga daga karfe takwas na dare zuwa bakwai na safe.
Gwarazan Yan Sanda Sun Ceto Mutum 8 da Yan Bindiga Suka Sace a Zamfara
A bangare guda, rundunar yan sanda reshen jihar Zamfara ta ceto mutum 8 da yan bindiga suka sace a ƙaramar hukumar Bungudu, jihar Zamfara kamar yadda Punch ta ruwaito.
Kakakin rundunar yan sandan jihar, ASP Muhammad Shehu, shine ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata a Gusau.
A cewarsa yan bindiga sun yi awon gaba da mutanen zuwa sansanin su dake Kungurmi, amma jami'ai sun ceto su cikin ruwan sanyi.
Asali: Legit.ng