Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna Akeredolu ya rattaba hannu kan dokar hana kiwo a fili

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna Akeredolu ya rattaba hannu kan dokar hana kiwo a fili

  • Gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo ya bi sahun wasu takwarorinsa na kudu ya rattaba hannu kan dokar hana kiwo a fili
  • Gwamna Akeredolu ya rattaba hannu kan dokar ne a ofishinsa da ke Akure a ranar Talata 31 ga watan Agusta
  • Donald Ojogo, kwamishinan watsa labarai na jihar Ondo ya ce dokar alheri ce ga jihar kuma za ta inganta zaman lafiya da tattalin arziki

Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na Jihar Ondo ya rattaba hannu kan dokar hana kiwo a fili da Majalisar Dokokin Jihar ta yi kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Daily Trust ta ruwaito cewa Akeredolu ya rattaba hannu kan kudirin dokar ne a ofishin sa da ke Akure, babban birnin jihar a ranar Talata.

Da Ɗumi-Ɗumi: Gwamna Akeredolu ya rattaba hannu kan dokar hana kiwo a fili
Gwamna Oluwarotimi Akeredolu na jihar Ondo. Hoto: Daily Trust
Asali: Facebook

Kara karanta wannan

An sassauta doka: Mazauna Jos sun garzaya kasuwanni domin sayen kayan abinci

Donald Ojogo, kwamishinan watsa labarai na jihar, ya ruwaito gwamnan na cewa:

"Matakin ya yi daidai ta matsayar da Kungiyar Gwamnonin Kudu suka cimma a taron su na ƙarshe da suka yi a Legas inda suka tsayar da ranar 1 ga watan Satumba a matsayin ranar karshe ga gwamnonin kudu su rattaba hannu kan dokar."
"Wannan doka ce mai kyau kuma abin yabawa da aka yi domin dakile rikici tsakanin mutane tare da tabbatar da mutanen Ondo sun cigaba da zama lafiya.
"Yana da kyau a gane cewa dokar za ta ƙarfafa zaman lafiya tsakanin mazauna jihar Ondo ba tare da la'akari da kabila ko addini ba. Ba a yi dokar don musgunawa wasu mutane ba.
"Yayin da gwamnati ke fatan mazauna jihar za su yi amfani da wannan dokar don haɓaka rayuwarsu ta yau da kullum, za mu tabbatar kowa ya bi dokar. Gwamnati za ta tabbatar an bi dokar.

Kara karanta wannan

Rikicin Jos: Wasu Migayu Ne Ke Amfani Da Addini Da Siyasa Don Ganin Ba a Zauna Lafiya Ba a Plateau, Lalong

"Don haka, za a fitar da cikakken bayani game da dokar saboda al'umma su fahimci abin da ta ƙunsa."

An dai daɗe ana cece-kuce game da batun saka dokar a jihohin kudu.

Wata jihar Nigeria za ta hana mutanen da ba suyi riga-kafin Korona ba shiga masallatai, coci da bankuna

A wani labarin daban, Gwamnatin jihar Edo ta ce za ta saka tsauraran matakai a bankuna, majami'u, masallatai da wuraren shagulgulan biki kan duk wanda bai nuna shaidar yin riga-kafin cutar korona ba daga watan Satumba.

Daily Trust ta ruwaito cewa, Gwamna Godwin Obaseki na jihar ya sanar da hakan ranar Litinin yayin kaddamar da kashi biyu na riga-kafin cutar korona a Benin City.

Ya ce cutar korona nau'in Delta na yaduwa sosai kuma tana cigaba da yaduwa a kowanne lokaci, lamarin da yasa dole jama'a su yi riga-kafin cutar, Daily Trust ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Shugaba Buhari: Zan yi maganin masu ta da hankali da kashe-kashe a Jos

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: