Raba-gari: A karshe Shugaba Buhari ya bayyana wadanda ke daukar nauyin IPOB

Raba-gari: A karshe Shugaba Buhari ya bayyana wadanda ke daukar nauyin IPOB

  • Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da ayyukan kungiyar nan mai neman ballewa ta Indigenous People of Biafra
  • Shugaban Najeriyan ya bayyana dalilin da ya sa ayyukan haramtaciyyar kungiyar ba shi da amfani
  • Buhari ya nuna kwarin gwiwar cewa Najeriya za ta ci gaba idan 'yan kasa ba su yarda su zama wakilan rabuwa ba

Abuja - Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, ya yi zargin cewa haramtaciyyar kungiyar nan ta Indigenous People of Biafra (IPOB) na samun goyon bayan wasu ‘yan kasashen waje da ake biyansu albashi mai tsoka.

Buhari ya yi wannan zargin ne a ranar Litinin, 30 ga watan Agusta, a cikin wata sanarwa da Garba Shehu, babban mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai ya fitar.

Kara karanta wannan

Da Dumi-Dumi: Sabuwar Kungiyar Yan Tada Ƙayar Baya Ta Bayyana a Yankin Kudu Maso Gabas

Raba-gari: A karshe Shugaba Buhari ya bayyana wadanda ke daukar nauyin IPOB
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah wadai da ayyukan 'yan IPOB Hoto: Femi Adesina
Asali: Facebook

Ya yi zargin cewa kungiyar tana aikata ayyukan ta’addanci ne domin satar kudi.

Buhari ya bayyana cewa IPOB ba gwagwarmayar neman 'yanci take yi ba yayin da suke kai hari kan ofisoshin 'yan sanda da kadarori.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Shugaban kasar ya yi watsi da hasashen cewa kungiyar na kare hakkin Kiristoci ne.

Ya ce:

''IPOB ba Kiristoci take karewa ba - kamar yadda masu fafutukarsu na kasashen waje da ake biya makudan kudade suke da'awa - a yayin da kusan dukka ‘yan asalin jihohin da suke addaba suka kasance Kiristoci ne.''

Shugaban kasar ya bayyana cewa masu fakewa a bayan 'yan kungiyar ne suka yaudare su.

Ya ce wasu kafofin watsa labarai na kasashen waje da 'yan siyasa sun yarda da labarin karyar na cewa IPOB tana wakiltar muradun Kiristoci ne.

Kara karanta wannan

Sabuwar Ƙungiyar APC Ta Buƙaci Buhari Ya Zaɓi Magajinsa Daga Kudu Maso Gabas

Shugaban kasar ya bukaci ‘yan Najeriya da su hada kai su yi adawa da wadanda ke kokarin haddasa rarrabuwar kawuna a kasar saboda son rai.

NDA: Babban malamin adddini ya aika gagarumin gargadi ga 'yan Najeriya, ya ce karin matsaloli na tafe

A wani labari na daban, daraktan cocin Adoration Ministry Enugu Nigeria, AMEN, Rev. Father Ejike Mbaka, ya aika da sakon gargadi ga ‘yan Najeriya.

Malamin ya fito fili ya bayyana cewa harin da aka kai a Kwalejin horon sojoji na Najeriya somin tabi ne na abin da zai riski Najeriya, jaridar Punch ta rahoto.

Don haka ya bukaci gwamnatin Muhammad Buhari da ta canza tare da yin kira ga Allah da ya shiga cikin harkokin kasar, idan ana son kawar da matsalar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng