Direba ya mayar da jakar da ya tsinta dauke da $20,000 ga mai ita a filin jirgin saman Legas

Direba ya mayar da jakar da ya tsinta dauke da $20,000 ga mai ita a filin jirgin saman Legas

  • Wani direban daya daga cikin motocin da ke jigilar fasinjoji daga filin saukar jirgin sama na Murtala Muhammad da ke Lagas ya nuna tsantsar gaskiya da amanarsa
  • Direban ya tsinci wata jaka da wani fasinja ya bari a motar wanda ke dauke da damin daloli da kayayyaki na miliyoyin nairori
  • Sai dai bai yi kasa a gwiwa ba wajen mika jakar ga sashin da ya kamata, inda aka gano mai ita tare da tuntubarsa domin mayar masa da abarsa

Lagas - An mayar da wata jaka da ke kunshe da daloli $ 20,000; N500,000, sarka da sauran abubuwa masu daraja na miliyoyin Nairori da aka manta da su a ɗaya daga cikin bas ɗin jigilar fasinjoji a filin jirgin sama na Murtala Muhammed da ke Lagas, ga mai shi.

Kara karanta wannan

Abinda ka raina: Ana sayar da jakar 'Ghana-Must-Go' N860k a Amurka

An gano cewa jakar mallakar wani fitaccen dan Najeriya ne (wanda aka sakaye sunansa) wanda ya hau jirgin kamfanin Arik Air daga Lagas zuwa Fatakwal, babban birnin jihar Ribas a ranar Litinin, Daily Trust ta ruwaito.

Direba ya mayar da jakar da ya tsinta dauke da $ 20,000 ga mai shi a filin jirgin saman Legas
Direba ya mayar da jakar da ya tsinta dauke da $ 20,000 ga mai shi a filin jirgin saman Legas Hoto: Daily Trust
Asali: UGC

Rahoton ya nuna cewa an mika jakar wadda wani jami’in tsaro na filin jirgin ya gani zuwa sashin BASL, ma’aikatan tashar.

Manajan da ke kula da harkokin kamfanin na BASL, Mikail Mumuni, wanda ya bayyana hakan, ya ce an manta da jakar ne a cikin doguwar motar da ake amfani da ita wajen jigilar fasinjoji daga bangaren saukar jirage, mai lamba BDG 689 GW.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An ce direban bas din, Mista Emmanuel Eluu ne ya tsinta jakar sannan kuma ya mika wa Babban Sufeton tsaro na AVSEC, Mista Taiwo Adelakun.

Mumuni ya ce:

“Eluu ya samu rakiyar Gbadamosi Olasunkami (mai kula da ayyuka na bangaren saukar jirgin) da Oluwole Alonge (Shugaban ayyuka na bangaren saukar jirgin) don tabbatar da abin da aka ajiye a cikin jakar da kuma kiyaye abun da ke ciki.”

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya ba DSS umarnin kame malamai masu wa'azi ba tare da izinin gwamnati ba

Mai magana da yawun BASL ya kara da cewa kayan da aka samu a cikin jakar sun hada da $20,000.00 bandir biyu, N500,000 bandir guda biyar, agogon hannu guda tara cikin jaka launin baki da rawaya, dutsen ado a cikin jaka launin rawaya, tabarau guda daya, sarka a cikin jaka mai launin ruwan gwal biyu, cak din banki guda hudu, da maganin ido.

Sauran kayayyakin sune takardar saka wasika iri daban daban, katin ciniki mallakin mai jakar (an sakaya sunaye), katin shaida da waya kirar Samsung Note 20 Ultra.

Ya ce Shugaban tsaron ya tuntubi mai jakar bisa umarnin Manajan AVSEC ta lambar wayar da ke kan katin kasuwancin.

Kakakin ya ce a lokacin da ya isa Fatakwal, mai jakar wanda ya hau jirgin Arik Air daga Lagas ya umurci hadiminsa ya karbo jakar a madadin sa.

Ya ce:

"Mai jakar ya fara tattaunawa da Adelakun (Shugaban Tsaro) ta bidiyo yana mai tabbatar da asalin hadiminsa kuma ya gode wa ma'aikatan MMA2 saboda gaskiya da kwarewar da suka nuna.”

Kara karanta wannan

Kwamishinan 'yan sanda ya ba da umarnin a binciko wadanda suka kashe dan sanata

A wani labarin, wani dan Najeriya, Obiefoh Sunday, wanda ke aikin goge-goge a otal din Lagos Continental, ya nuna gaskiya a aikinsa.

Maigidansa, Muhammad Ashraf, a shafinsa na LinkedIn ya rubuta game da yadda saurayin ya samo wasu daloli na Amurka a daya daga cikin dakunan da ya je tsabtacewa bayan bakon da ya sauka a ciki ya tafi.

Yana tsintar kudin, nan take sai mai aikin goge-gogen ya sanar da hukumar otal din halin da ake ciki kuma an hanzarta shigar da kudin cikin asusun kungiyar kudaden da aka rasa masu shi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel