Kwamishinan 'yan sanda ya ba da umarnin a binciko wadanda suka kashe dan sanata
- Kwamishinan 'yan sanda a jihar Kaduna ya ba da umarnin a kamo wadanda suka kashe dan sanata Bala Ibn Na-Allah
- A jiya ne 'yan ta'adda suka haura gidan dan sanatan inda suka makure shi har ya bakunci lahira
- Lamarin ya faru ne yayin da lamurran tsaro ke kara ta'azzara a arewacin Najeriya, musamman arewa maso yamma
Kaduna - Rahoton da ya fito daga jaridar Punch ya bayyana cewa, kwamishinan 'yan sanda a jihar Kaduna, Mudasiru Abdullahi ya ba da umarnin fara cikakken bincike don gano wadanda suka aikata ta'asar kashe dan sanata Bala Ibn Na-Allah.
A jiya ne muka samu rahoto daga majiyoyi daban-daban kan cewa, an shiga gidan wani matukin jirgin sama, kuma dan sanata mai ci a jihar Kebbi Abdulkarim Ibn Na-Allah, inda aka makure shi aka hallaka shi a cikin gidansa.
A wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na hukumar 'yan sanda, ASP Muhammad Jalige ya fitar ya bayyana umarnin da kwamishina ya bayar bayan tabbatar da faruwar lamarin.
A cewar sanarwar da take bayyana kalaman kwamishinan:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Na ba da umarnin a gudanar da cikakken bincike da nufin bankado masu laifin da kuma gurfanar da su gaban kuliya.
"Rahoto ya nuna cewa masu kisan sun yi nasarar shiga gidan matukin jirgin a Titin Umar Gwandu, Malali, Kaduna cikin dare, suka makure shi har lahira cikin ruwan sanyi sannan suka tafi da motar sa kirar Lexus SUV zuwa inda ba a sani ba."
Rundunar 'yan sandan ta yi kira ga jama'a da su taimaka da bayanai masu amfani da za su taimaka wajen gudanar da bincike kan kisan.
Yadda aka je har gida, aka makure babban dan Sanata Na-Allah, inji Gwamnatin Kaduna
Rahoton da Daily Trust ta fitar, ya bayyana cewa gwamnatin jihar Kaduna ta yi magana a game da mutuwar ‘dan Sanata Bala Ibn Na’Allah. Gwamnatin Kaduna ta ce wani ne ya kashe Kyaftin Abdulkarim Na-Allah ta hanyar shake masa wuya.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan ya fitar da jawabi, yace jami’an tsaro sun sanar da su game da mutuwar.
Da yake jawabi a yammacin Lahadi, Samuel Aruwan yace mutuwar ta yi kama da kisan-kai, inda aka makure marigayin da igiya, har yace ga garinku nan.
'Yan ta'adda sun kutsa gidan dan sanatan Kebbi a cikin gidansa, sun hallakashi
A baya mun ruwato muku cewa, an gano gawar babban dan Sanata Bala Na Allah, Kyaftin Abdulkarim Bala Na Allah, a dakin kwanansa da ke Malali a jihar Kaduna.
Daily Trust ta tattaro cewa matukin jirgin mai shekaru 36, wanda ya yi aure kwanan nan, an daure shi kuma kana aka shake shi har ya mutu yayin da maharan suka tsere da motarsa da kayayyakinsa.
Mai ba da shawara na musamman ga Sanata Na Allah, Garba Mohammed, yayin tabbatar da mummunan abin da ya faru, ya ce maharan sun samu shiga gidan ne ta rufin bayan gidansa.
Asali: Legit.ng