Zulum Ya Ziyarci Faston Da Aka Kashe Ɗansa Yayin Rushe Coci a Borno Don Masa Ta'aziyya

Zulum Ya Ziyarci Faston Da Aka Kashe Ɗansa Yayin Rushe Coci a Borno Don Masa Ta'aziyya

  • Gwamnan Borno Babagana Zulum ya ziyarci fasto Bitrus Tamba da aka kashe dansa a Maiduguri
  • Ezekiel Bitrus ya rasu ne sakamakon harbinsa da jami'an tsaro suka yi yayin zanga-zangan da suka yi lokacin da ake rushe coci
  • Zulum ya jadada wa Fasto Tamba cewa wadanda suka yi harbin suna tsare kuma za a hukunta su idan an kammala bincike

Babagana Zulum, gwamnan jihar Borno ya ziyarci Bitrus Tamba, faston da aka kashe dansa yayin rushe cocin Ekklesiyar Yan’uwa Nigeria (EYN) da ke Maiduguri, babban birnin jihar, The Cable ta ruwaito.

Ezekiel Bitrus, dan faston na daga cikin wadanda suka yi zanga-zangar nuna kin amincewarsu da rushe cocin da hukumar BOGIS ta jihar Borno ta yi a watan Agusta.

Zulum Ya Ziyarci Faston da Aka Kashe Ɗansa Yayin Rushe Coci a Borno
Gwamnan Borno Babagana Zulum yayin da ya ziyarci Fasto Bitrus Tamba a gidansa da ke Maiduguri. Hoto: The Cable
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Tsohon gwamnan Neja: Dole ne a ilmantar da 'yan Najeriya idan ana son bindiganci ya kare

A cewar rahoton na The Cable, jami'an tsaro da suka taho tare da BOGIS sun bude wa masu zanga-zangan wuta da nufin tarwatsa su amma harsashi ta samu Bitrus.

Yayin ziyarar da ya kai masa a gidansa a daren ranar Talata, Zulum ya bayyana mutuwar a matsayin 'abin da ba a so ba'.

Jawabin Zulum a gidan Fasto Tamba

Gwamnan ya ce:

"Zan fara da neman afuwa saboda jinkirta ziyara ta duk da cewa na turo wakilai na su yi maka bayani. Mun jinkirta ziyarar ne saboda yanayin dar-dar a garin. Munyi tunanin ba wannan lokacin ya kamata mu kawo ziyarar ba."
"Na zo nan ne domin yin ta'aziyya gare ka da iyalanka bisa mutuwar dan uwanmu Ezekiel Bitrus. Zuwa na nan, makonni bayan afkuwar abin mara dadi, alama ce da ke nuna ba mu manta da lamarin ba."

Zulum ya ce wadanda suka yi harbin suna tare kuma za a hukunta su idan yan sanda sun kammala bincikensu kan lamarin.

Kara karanta wannan

'Yan ISWAP sun fatattaki mazauna daga gidajensu a jihar Borno zuwa kasar Kamaru

Abin da faston ya ce?

A bangarensa, faston ya yi wa gwamnan godiya bisa ziyarar da ya kai masa.

Tumba ya ce:

"Duk abin da za mu yi, ba za mu iya dawo da wanda ya mutu ba; a matsayin mu na kirista na gari, mun rungumi kaddara.
"Muna godiya ga mai girma gwamna bisa ziyarar, ina bibiyar dukkan kokarin da ka ke yi kan rasuwar dan mu kuma tabbas baka manta da mu ba, muna godiya matuka."

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel