An kai hari NDA ne kawai don batawa gwamnatin Buhari suna, Mai magana da yawun shugaban kasa
- Femi Adesina ya saki dogon jawabi kan harin da yan bindiga suka kai makarantar NDA
- Yan bindiga sun kai mumunar farmaki jami'ar horar da Sojojin Najeriya NDA
- Yayinda suka hallaka jami'an Sojoji biyu da jikkata daya, sun yi awon gaba da Manjo daya
Abuja - Mai magana da yawun shugaban kasa, Mr Femi Adesina, ya bayyana cewa an kai hari makarantar horon Soji NDA ne domin nuna cewa gwamnantin Buhari ta gaza.
A cewarsa, yan bindiga sun shiga NDA ne don rage azamar Sojoji dake yaki da su.
Adesina ya bayyana hakan ne jawabin da ya daura kan shafinsa na Facebook ranar Alhamis.
Yace dukkan masu kokarin batawa Sojojin Najeriya suna marasa godiya ne.
Yace:
"Abinda ya faru a makarantar Sojoji, me manufar hakan? Abu mai sauki ne. Da gayya aka kai harin domin batawa gwamnati suna, da kuma ragewa Sojoji karfin gwiwa a daidai lokacin da suke fama da matsalar rashin tsaro."
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Wasu masu sharhi zasu zo da maganganun karya, jam'iyyun hamayya da kungiyoyi masu bakin ciki zasu rika yadawa, kamar sammai zasu rikito. Wasu irin mutane ne yan kasar nan? Marasa godiya, marasa daraja."
Garba Shehu: Babu mamaki ‘Yan bindiga sun aukawa NDA ne da nufin a bata wa Buhari suna
Hakazalika Garba Shehu, yace harin da aka kai a makarantar sojoji na iya zama shiri da nufin bata sunan shugaba Muhammadu Buhari.
Malam Garba Shehu ya yi wannan magana ne a lokacin da ‘yan jarida su ka yi hira da shi a gidan talabijin Channels TV a ranar Laraba, 25 ga watan Agusta, 2021.
Mai magana da yawun shugaban kasar yace Mai girma Muhammadu Buhari yana sa rai sojoji su bincika, su gano ainihin abin da ya faru, a shaida wa Duniya.
Ya aka yi 'Yan bindiga suka shiga NDA?
An samu labari barci ya ci karfin sojojin da aka tanada a dakin CCTV a lokacin da abin ya faru Hakan ya sa ‘Yan bindiga su ka shiga makarantar sojojin, suka yi ta’adi.
Rahotanni sun ce idan hakan ta tabbata, za a hukunta sojojin da barci ya dauke a bakin aiki. Daga baya an ji cewa hedikwatar tsaro ta kasa ta musanya wannan rahoton.
Asali: Legit.ng