Kashe-Kashen Jos: CAN ta miƙa muhimman saƙo ga shugabannin musulmi da kirista a Plateau

Kashe-Kashen Jos: CAN ta miƙa muhimman saƙo ga shugabannin musulmi da kirista a Plateau

  • Kungiyar CAN ta roki shugabannin musulmi da kirista su guji tunzura magoya bayansu a Plateau
  • Kungiyar ta isar da wannan sakon ne cikin wata sanarwa da shugabanta da sakatarenta suka fitar
  • CAN ta ce yanzu lokaci ne da ya dace shugabannin addini su rika wa'azin zaman lafiya da hadin kai

Kungiyar kirista ta Nigeria, CAN, a Jos, babban birnin jihar Plateau ta roki shugabannin musulmi da na kirista su dena tunzura mutane suna miyagun ayyuka, Peoples Gazette ta ruwaito.

A cewar sanarwar da ta fitar a garin Jos a ranar Laraba mai dauke da sa hannun shugaban CAN, Polycarp Gana da satare Ezekiel Noam, kungiyar ta kuma yi Allah wadai da kashe-kashen da aka yi a Yalwan Zangam.

Kara karanta wannan

Hawaye sun kwaranya sakamakon kashe tsohon ɗan kwallon Nigeria da aka yi a rikicin Jos

Kashe-Kashen Jos: CAN ta miƙa muhimman saƙo ga shugabannin musulmi da kirista a Plateau
Tasiwirar Jihar Plateau. Hoto: Vanguard NGR
Asali: Twitter

Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun afka garin a daren ranar Talata sun kashe mutane masu yawa sannan suka kona gidaje da dama.

CAN ta shawarci shugabannin addini a Plateau su guji furta kalaman da ka iya tunzura mutane ko tada rikici.

Sanarwar ta ce:

"Muna Allah-wadai da kashe-kashen da aka yi wa mutanen da ba su-ji-ba ba-su-gani-ba a gidajensu a Yalwa Zangam. Wannan abin bakin ciki ne da takaici da damuwa.
"Muna kira ga malamai a jihar su guji furta kalamai da za su iya tunzura al'umma amma su rika yin wa'azin zaman lafiya, fahimtar juna, da hadin kai tsakanin mutane."

Rahoton na Peoples Gazette ya kuma ce kungiyar ta bukaci shugabannin addini su dena furta kalaman da za su iya tada zaune tsaye a wannan lokacin da ya dace su rika kwantar da hankulan mutane daga ayoyin littafan su a maimakon ta'azzara lamarin.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan bindiga suka sace ɗalibin NDA kuma ɗan alƙali a Kaduna

Kungiyar ta yaba wa hukumomin tsaro bisa kokarinsu na ganin an tabbatar da zaman lafiya a jihar suna kuma bukatar su kara zage damtse.

Yayin da ta ke mika sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda abin ya shafa, kungiyar addinin ta shawarci mutane su dage da addu'a su kuma kame bakinsu daga furta kalamai da ka iya tada hankula.

Ta bukaci mutane su cigaba da sa ido kan abin da ke kaiwa da kawowa a unguwanninsu su sanar da hukumomin tsaro idan sun ga abin da ba su gamsu da shi ba.

Kashe-kashen Plateau: An yi ram da mutum 10, Lalong ya shiga taron tsaro na gaggawa

A wai labarin daban, kun ji an kama mutane 10 da suke da alaka da kai sabon hari kauyen Yelwa Zangam na Jos ta arewa da ke jihar Filato, Daily Trust ta ruwaito hakan.

Gwamna Simon Lalong ya kwatanta harin a matsayin rashin imani, sannan ya shirya taro na gaggawa don tattaunawa da kuma neman hanyar kawo garanbawul ga kashe-kashen da aka maimaita a jiharsa.

Kara karanta wannan

Kisan gilla a Jos: Hukuma taci alwashin kame mazauna yankunan da ake kashe-kashe

A wata takarda wacce darektan watsa labarai ya saki, Makut Mechan, ya ce gwamnan ya umarci jami’an tsaro su binciko duk wadanda suke da hannu a lamarin da masu daukar nauyinsu don a hukunta su.

Asali: Legit.ng

Online view pixel