'Yan jaridan Channels TV 2 sun kwashe sa'o'i a hannun jami'an DSS kan tattaunawar sukar Buhari
- Mai'aikatan gidan talabijin na Channels TV 2, Chamberlain Usoh da Kayode Okikiolu sun kwashe sa'o'i a hukumar DSS
- An gano cewa hukumar ta gayyacesu a ranar Alhamis tun bayan tattaunawar da suka yi da Gwamna Ortom na jihar Benue
- Gwamnan ya yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari wankin babban bargo, lamarin da yasa fadar shugaban kasa ta yi masa tatas
FCT, Abuja - Jami'an hukumar DSS sun titsiye 'yan jarida 2 na gidan talabijin na Channels masu suna Chamberlain Usoh da Kayode Okikiolu, na tsawon sa'o'i a ranar Alhamis kan tattaunawa da suka yi da Gwamna Samuel Ortom na jihar Benue wacce suka yi a ranar Talata.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, daga bisani jami'an tsaron na sirri sun sako 'yan jaridan wurin karfe 7 na yamma.
Jami'in DSS ya warware zare da abawa
Wani babban jami'i a hukumar ya sanar da Daily Trust cewa, an gayyesu ne sakamakon wani korafi da hukumar watsa labarai ta kasa, NBC ta mika musu.
An tattaro cewa, hukumar ta bincike su ne kan wata tattaunawa da suka yi da Navy Commodore Kunle Olawunmi, wanda ya zargi cewa akwai masu daukar nauyin Boko Haram a mukarraban Buhari.
Jami'in ya kara da cewa, masu gabatarwan wadanda suka samu rakiyar lauyansu, an tuhumesu ne kan yadda suka bar gwamna ba tare da sun kwaba masa ba, inda ya dinga miyagun kalamai.
Ya kara da cewa, kafin a sako su a daren jiya, an bukace su da su yi alkawarin cewa hakan ba zai sake faruwa ba nan gaba.
Sai dai su biyun sun ki daukan wannan alkawarin inda suka ce aiki kadai gidan talabijin din ta daukesu, don haka ba su da wata dama ta daukar wani alkawari a madadin kamfanin.
Mai magana da yawun 'yan sandan sirrin, Peter Afunanya, ya musanta damke 'yan jaridan, amma kuma bai sanar da cewa ko da gaske bane gayyatarsu da aka yi.
"Wannan karya ne kuma shirme ne. Masu yada labaran bogi sun ki tuba," Afunanya yace a wata takarda da ya mika ga manema labarai a daren jiya.
Zargin takardun bogi: Kotu ta ki kwace kujerar mai magana da yawun majalisar wakilai
A wani labari na daban, babbar kotun jihar Abia ta yi fatali da karar da Okey Ezeala ya mika a kan kakakin majalisar wakilai, Benjamin Kalu. Ezeala ya zargi Kalu da amfani da takardun makaranta na bogi.
Kamar yadda Daily Trust ta ruwaito, mai karar ya yi ikirarin cewa akwai canjin suna a takardun makarantarsa.
A wani hukunci da alkali A.O. Chijioke ya yanke, ya ce zargin da ake yi wa Kalu bashi da tushe balle makama.
Asali: Legit.ng