Amurka ta gama ficewa daga Afghanistan, jirgin karshe ya tashi ranar Litinin

Amurka ta gama ficewa daga Afghanistan, jirgin karshe ya tashi ranar Litinin

  • Hukumonin Amurka sun kammala janye wa a kasar Afghanistan kamar yadda suka alkawarta a baya
  • Jirgin karshe dake jigilar kwashe Amurkawa da kawayensu da suka taimaka musu a Afghanistan sun tashi jiya Litinin
  • Sai dai, wasu rahotanni na cewa, Amurka ta bar wasu daga cikin mutanenta da kawayenta a kasar ta Afghanistan

Afghanistan - Hukumomin Amurka a ranar Litinin, 30 ga watan Agusta sun sanar da cewa dukkan dakarunta sun fice daga kasar Afghanistan.

Jaridar Fox News ta ba da rahoton cewa jirgin C-117 na karshe dauke da membobin aiki na Amurka ya tashi daga filin jirgin saman Kabul da misalin karfe 3:29 na yamma agogon Amurka.

Fadar White House ta ce a cikin awanni 24 daga safiyar Lahadi, 29 ga Agusta zuwa Litinin, Amurka ta kwashe mutane 1,200 daga Kabul, tare da jiragen soji 26 da jiragen hadin gwiwa guda biyu dauke da wadanda suka fice daga kasar Afghanistan.

Kara karanta wannan

Bayan da Taliban ta karbe mulkin Afghanistan, Amurka ta kai hari da jirgi

Afghanistan: Jirgin karshe mai kwashe Amurkawa ya tashi a Kabul
Shugaban Kasar Amurka, Joe Biden | Hoto: theguardian.com
Asali: UGC

Jirgin sama na karshe daga Kabul ya tashi

Ficewar Amurka ta karshe ta zo ne sa'o'i kafin ranar Talata, 31 ga watan Agusta da Shugaba Joe Biden ya kaddara.

Ficewar da aka yi cikin dar-dar din hare -haren ta’addanci ya yi sanadiyyar mutuwar ma’aikatan Amurka 13 da kuma ‘yan Afghanistan fiye da 200.

Jaridar Wall Street Journal ta ba da rahoton cewa duk da tabbacin da Biden da sauran manyan jami'an gwamnati suka bayar na kwashe kowa, an bar Amurkawa da kawayen Afghanistan, duk da cewa Ma'aikatar Harkokin Wajen ba ta iya ba da takamaiman adadinsu ba.

Sky News ta ba da rahoton cewa an ji karar harbin bindiga a kusa da Kabul jim kadan bayan jirgin na karshe ya tashi.

Ku tuna cewa jirgin saman Amurka mara matuki ya kai hari a ranar Lahadi, 29 ga watan Agusta kan wata mota a Kabul dauke da abubuwan fashewa.

Kara karanta wannan

Da dumi-dumi: An harbe mutum 11 har lahira a sabon harin da aka kai Katsina

Babban hafsan sojojin ruwan Amurka Bill Urban ya fada a cikin wata sanarwa cewa harin ta sama ya kawar da barazanar ISIS-K da ke gab da faruwa.

Bayan da Taliban ta karbe mulkin Afghanistan, Amurka ta kai hari da jirgi

A wani labarin, sojojin Amurka sun kai hari da jirgi mara matuki kan wani mutum da ta ce mai shirin kunar bakin wake ne na ISIS-K a lardin Nangarhar da ke gabashin Afghanistan, a yayin da ake gargadin yiwuwar kai sabbin hare-hare wajen kokarin kwashe Amurkawa daga Kabul.

Manufar yunkurin jigilar kwashe Amurkawa da 'yan Afghanistan wadanda suka taimaka wa sojojin Amurka da jami'ai daga kasar zuwa karshen watan nan ya zo karshe.

A cewar mazauna yankin da aka kai harin a daren Juma'a, akalla mutane uku sun mutu - namiji, mace da yaro - kuma mutane da dama sun jikkata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.