Buhari ya yiwa 'yan bindiga masu AK-47 abun da ya fi ayyana su a matsayin 'yan ta'adda muni, Garba Shehu

Buhari ya yiwa 'yan bindiga masu AK-47 abun da ya fi ayyana su a matsayin 'yan ta'adda muni, Garba Shehu

  • Fadar shugaban kasa ta magantu kan kokarin da gwamnati mai ci ke yi wajen yaki da masu tayar da kayar baya da fashi da makami a kasar
  • Malam Garba Shehu ya ce "ana samun nasarori masu yawa" a yaki da ta'addanci a fadin kasar
  • Da yake zantawa da BBC Pidgin a ranar Asabar, Shehu ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wa 'yan fashi abu mafi muni fiye da tunanin kowa

Abuja - Garba Shehu, hadimin shugaban kasa kan harkokin yada labarai, ya bayyana cewa ana samun “manyan nasarori” a cikin yaki da gwamnatin tarayya ke yi da ‘yan fashi da masu ta’addanci.

Shehu ya bayyana hakan ne da safiyar Asabar, 28 ga watan Agusta, yayin wata hira da BBC Pidgin wanda Legit.ng ta sanya ido.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa ta yi barazanar hukunta jami'an da aka samu da cin amana

Buhari ya yiwa 'yan bindiga masu AK-47 abun da ya fi ayyana su a matsayin 'yan ta'adda muni, Garba Shehu
Garba Shehu ya bayyana kokarin gwamnati na ganin bayan masu tayar da kayar baya Hoto: All Progressives Congress (APC)
Asali: Facebook

A cewarsa, an yi watsi da nasarorin da aka samu a yaki da ta’addanci, fashi da makami da sauran laifuka.

Ya kara da cewa an kara himma don tabbatar da cewa sojojin Najeriya sun sami nasara cikin sauri kan masu kera muggan makamai.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari ya muzanta wa 'yan fashi

Da yake tabbatar da kokarin da gwamnati mai ci a yanzu ke yi na yaki da miyagun laifuka da ta’addanci, Garba Shehu ya ce gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari “ta yi wa ‘yan bindigar da ke dauke da makamai abun da ya fi ayyana su a matsayin ‘yan ta’adda muni.”

Hadimin shugaban kasar ya ce umurnin da Buhari ya bayar na harbe 'yan bindigar da aka gani da AK-47 bai kai kan kungiyar da aka haramta na Indigenous People of Biafra (IPOB) ba.

Kara karanta wannan

Garba Shehu: Babu mamaki ‘Yan bindiga sun aukawa NDA ne da nufin a bata wa Buhari suna

Shehu ya ce ba a yiwa ‘yan bindiga rikon sakainar kashi ba-dalilin kenan da yasa sojojin Najeriya ke tayar da bama-bamai a wurarensu, sannan sojin kasa na musayar wuta da su.

Garba Shehu: Babu mamaki ‘Yan bindiga sun aukawa NDA ne da nufin a bata wa Buhari suna

A wani labarin, Hadimin shugaban Najeriya, Garba Shehu, yace harin da aka kai a makarantar sojoji na iya zama shiri da nufin bata sunan shugaba Muhammadu Buhari.

Malam Garba Shehu ya yi wannan magana ne a lokacin da ‘yan jarida su ka yi hira da shi a gidan talabijin Channels TV a ranar Laraba, 25 ga watan Agusta, 2021.

Mai magana da yawun shugaban kasar yace Mai girma Muhammadu Buhari yana sa rai sojoji su bincika, su gano ainihin abin da ya faru, a shaida wa Duniya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel