Hotunan Gidan da Aka Tsinci Gawar Babban Ɗan Sanatan APC a Kaduna

Hotunan Gidan da Aka Tsinci Gawar Babban Ɗan Sanatan APC a Kaduna

  • Wasu da ba'a gano ko suwaye ba sun kutsa cikin gidan babban ɗan sanata Bala Na'Allah suka kashe shi a Kaduna
  • Maharan sun tattara wasu muhimman kayayyakinsa tare da motarsa sun tafi da su
  • Rahoto ya nuna cewa maharan sun samu damar shiga gidan ne ta rufin kwano, inda suka isa dakinsa ta silin

Kaduna - A ranar Lahadin nan da muke ciki ne aka tsinci gawar babban ɗan sanata Bala Na Allah, Abdulkarim Bala Na Allah, a ɗakin kwanansa dake unguwar Malali cikin garin Kaduna.

Dailytrust ta ruwaito cewa Abdulkarim Na Allah, ɗan kimanin shekara 36 a duniya matukin jirgin sama ne, kuma bai jima da yin aure ba.

Legit.ng Hausa ta kawo muku rahoton cewa maharan da suka aikata wannan aika-aika sun tafi da motarsa da kuma wasu kayayyaki.

Kara karanta wannan

Mutum biyu sun mutu, yayin da Sojoji suka ragargaji Yan bindiga suka kubutar da matafiya a Kaduna

Hitunan gidan a Malali Kaduna

Hoton gidan a Malali
Hotunan Gidan da Aka Tsinci Gawar Babban Ɗan Sanatan APC a Kaduna Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Gidan yana Malali Kaduna
Hotunan Gidan da Aka Tsinci Gawar Babban Ɗan Sanatan APC a Kaduna Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Gidan da aka kashe ɗan sanata a Kaduna
Hotunan Gidan da Aka Tsinci Gawar Babban Ɗan Sanatan APC a Kaduna Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Yadda lamarin ya faru

Duk da cewa har yanzun hukumomi ba su fitar da sanarwa kan faruwar lamarin ba, amma kakakin Sana Na'Allah, Alhaji Garba Muhammed, yace makasan sun shake masa wuya ne har ya mutu, kamar yadda vanguard ta ruwaito.

Muhammed yace:

"Waɗanda suka aikata kisan sun tafi da mitarsa da wasu kayayyakinsa. Kuma sun shiga gidansa ne rufin kwano, sanna suka isa ɗakinsa da silin."
"Mai gadin gidan dake makotaka da na shi ne ya fahinci am buɗe babbar kofar gidan, nan take ya sanar da mutane."

A wani labarin kuma Mutum biyu sun mutu, yayin da Sojoji suka ragargaji Yan bindiga suka kubutar da matafiya a Kaduna

Dakarun soji na Operation Safe Haven sun sami nasarar kuɓutar da wasu matafiya uku da motar su daga hannun yan bindiga.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun kutsa gidan dan sanatan Kebbi a cikin gidansa, sun hallakashi

Rahoto ya nuna cewa maharan sun yi kokarin sace matafiyan ne a kan hanyar Gidan Waya zuwa Godogodo.

Asali: Legit.ng

Online view pixel