Rahoto: Bincike ya nuna irin sassaucin da za a yiwa Abba Kyari amma zai fuskanci kora
- Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan zargin Abba Kyari da hannu cikin aikata zamba, an fara hasashen makomarsa
- Bincike ya bayyana cewa, akwai yiyuwar a kori Abba Kyari daga aikin dan sanda ko a rage matsayinsa zuwa kasa
- Hakazalika, zai iya samun sassauncin da ba za a mika shi ga hukumomin kasar Amurka ba duba da wasu dalilan diflomasiyya
Akwai kwararan hujjoji da ke nuna cewa Abba Kyari dake fuskantar gurfana a Kotun Gundumar California ta Amurka bisa zarginsa da hannu a wata damfara ta shahararren dan damfara, Ramon Abbas (Hushpuppi), na iya samun sassaucin hukunci daga hukuma, in ji jaridar This Day.
Abba Kyari, wanda ya kasance mataimakin kwamishinan 'yan sanda kuma shugaban shugaban wata rundunar fikira ta IRT a Najeriya.
An dakatar da Abba Kyari yayin da aka fara gudanar bincike kan lamurran da suka faru tsakaninsa da Hushpuppi.
Bincike ya bayyana cewa, ana kyautata zaton Kyari ba zai dawo aikin dan sanda ba, amma zai iya samun sassaucin hukunci daga hukumomi, wanda daga cikin sassaucin shine; hukumar 'yan sanda ba za ta mika shi ga hukumomin kasar Amurka ba.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
This Day ta tattaro cewa yayin da akwai kwararan alamu na cewa Sufeto Janar na 'yan sanda (IG) na iya bayar da shawarar a sauke Kyari daga mukamansa, Hukumar Kula PSC za ta zabi a sallamarsa gaba daya saboda girman laifin nuna rashin da'a ga aikin 'yan sanda.
Yadda aka kafa kwamitin binciken kan Abba Kyari da goyon bayan da yake samu
Mataimakin Sufeto-Janar na 'yan sanda (DIG) Joseph Egbunike ya jagoranci kwamitin da IG ya kafa don binciken zargin da aka yi wa Kyari, a ranar Alhamis 26 ga watan Agusta ya mika rahotonsa ga IG, Usman Baba. An kafa kwamitin ne a ranar 2 ga Agusta, 2021.
Kafa kwamitin ya biyo bayan gurfanar da Kyari a wata karar da ta shafi Hushpuppi, wanda ke da hannu a damfarar $1.1m kan wani dan kasuwa na kasar Qatar a Kotun Gundumar Amurka ta California.
An tattaro cewa hukumomin da abin ya shafa suna shirin baiwa jami'in da aka gurfanar sassauncin hukunci.
Akwai kuma kungiyoyin goyon daga arewa dake kare Kyari. Hakazalika akwai lauyoyi da dama daga Arewa da suka bayyana kudurin kare Kyari a kotu.
An kuma tattara cewa IG, wanda da farko aka umarce shi da ya dakatar da Kyari tare da bincikar zarge-zargen da ake yi masa, kwanan nan ya sami karin umarni kan matakan da za a bi kan lamarin bayan gabatar da rahoton.
Majiyoyi sun bayyana abin da zai iya biyo bayan rahoton binciken Kyari
Bayan karbar rahoton, wasu majiyoyi daga hukumar 'yan sanda sun bayyana a karshen mako cewa:
“Suna iya yi masa sassaucin hukunci amma da alama ba zai koma aikin dan sanda ba. Hakanan akwai yuwuwar ba da izinin diflomasiyya don ba shi kariya.
“IG da shugaban PSC sun kuma sami umarnin kan abin da za su yi a lamarin. Wannan lamarin ba irin na cikin gida ne da za su iya magance shi su kadai ba.”
Wata majiya mai inganci kuma ta ce saboda rawar da Kyari ya taka wajen dakile aikata manyan laifuka, IG na iya bayar da shawarar a rage masa matsayi.
Sai dai hukumar kula da ayyukan ‘yan sanda, wacce ke da matsayi mai karfi kan duba hukuncin ladabtarwa, ana sa ran za ta dage kan korarsa gaba daya.
Jami'in hulda da jama'a na rundunar, Mista Frank Mba, a cikin wata sanarwa a ranar Laraba, ya ce Sufeto-Janar na 'yan sanda, Usman Baba cewa:
"Ya samu rahoton kwamitin bincike na musamman na NPF (SIP) da ke binciken tuhumar da ake yi a Kyari ta Ofishin Bincike na Tarayya (FBI) ”.
Batun Abba Kyari: Kwamiti ya gama bincike, ya mika rahoto ga Sufeto-Janar
A wani labarin, Kwamitin Bincike na Musamman ya mika rahotonsa ga Sufeto Janar na 'yan sanda, Usman Baba, makonni biyu bayan da aka umarce shi da ya binciki tsohon Shugaban rundunar IRT kuma Mataimakin Kwamishinan' Yan sanda, Abba Kyari.
Kwamitin na mutum hudu karkashin jagorancin Mataimakin Sufeto -Janar na 'yan sanda mai kula da sashin binciken manyan laifuka na rundunar, Joseph Egbunike, ya mika sakamakon binciken ga IG ranar Litinin 16 ga watan Agusta.
A baya mun rahoto cewa, hukumar FBI ta kasar Amurka ta zargi Abba Kyari da hannu cikin wata damfara da Abbas Ramon (Hushpuppi) ya yi kan wani dan kasuwar Qatar, Punch ta ruwaito.
Asali: Legit.ng